Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika sakon taya murna ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, yayin da yake bikin cikar shekarar haihuwarsa a ranar 21 ga Oktoba, 2025.
A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da Sanata Kwankwaso ya bayar wajen ci gaban ƙasa ta fannoni daban-daban, ciki har da kasancewarsa Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai a zamanin jamhuriya ta uku da Ministan Tsaro da Gwamnan Jihar Kano sau biyu, da kuma Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya.
Shugaban ƙasa ya bayyana cewa, tasirin siyasar Kwankwaso a Arewacin ƙasar, musamman a Kano, na nuni da irin siyasar jin ƙai da kishin jama’a da ya gada daga marigayi Malam Aminu Kano da marigayi Alhaji Abubakar Rimi.
An Fara Binciken Wani Tsohon Gwamna Kan Zargin Daukar Nauyin Yiwa Tinubu Juyin Mulki
“Sanata Kwankwaso aboki ne kuma abokin aiki wanda muka yi aiki tare a majalisar dokoki ta tarayya a shekarar 1992, sannan muka zama gwamnoni a shekarar 1999. Mun kuma yi aiki tare wajen kafa jam’iyyar APC. Ko da yake daga baya ya bar jam’iyyar don kafa NNPP, abin lura ne cewa har yanzu yana cikin tafiyar ci gaba,” in ji Shugaba Tinubu.
A daidai lokacin da ake ta jita-jita game da yiwuwar sabuwar dangantaka ko sauya sheka tsakanin manyan ‘yan siyasa, masu lura da al’amura sun bayyana sakon na Tinubu a matsayin alamar gina gada da kuma ƙarfafa zumunta a siyasa.
Shugaban ƙasa ya yi wa Sanata Kwankwaso fatan alheri, lafiya, da ƙarin shekaru masu amfani ga ƙasa da al’umma.