Kungiyar ’Yan Jaridun Kano ta Arewa ta godewa Gwamna Abba bisa ɗaukar nauyin ɗan jarida da ya yi Hatsari

Date:

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano ta Arewa ƙarƙashin jagorancin Kwamared Sha’aibu Sani Bagwai, ANIPR, ta bayyana godiyarta ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ɗaukar nauyin Rashin lafiyar ɗaya daga cikin ’yan kungiyar, Malam Lawan Isa Bagwai (LIB) ma’aikaci a gidan Radio Kano.

A cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar, Abdulmumin Abubakar Tsanyawa, ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24, ya ce kungiyar ta bayyana cewa yadda gwamna Abba ya yi gaggawar ɗaukar nauyin jinyar Malam Lawan bayan mummunan haɗarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyarsa ta zuwa aiki, ya nuna shi jagora ne Mai tausayi da jin kan al’ummarsa.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin aikin tiyatar kwakwalwa da aka yi masa a asibitin Prime Alliance Hospital da ke Tarauni, wanda hakan ya sa ya sami sauƙi sosai.

Kungiyar ta ce wannan aikin alheri ya sake tabbatar da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf na da gaske wajen kula da walwalar al’umma, ciki har da ma’aikatan kafofin yada labarai waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...

Kananan Hukumomin Tarauni Rogo da Doguwa sun zamo koma baya wajen yin rijistar Masu zabe a Kano

Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa yanzu kananan hukumomin...