Kamfanin Dala Inland Dry Port Ya Karyata Rahotannin Da Ke Danganta Iyalan Ganduje Da Mallakar Wani Sashi Na Kamfanin

Date:

Kamfanin Dala Inland Dry Port (DIDP) ya karyata rahotannin da ke cewa iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, suna da hannun jari ko wani nau’in mallaka a kamfanin.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Kamfanin, Barr. Adamu Aliyu Sanda, ya fitar ranar Laraba, kamfanin ya bayyana rahotannin a matsayin “karya, rudani, da kuma abun da ke cike da siyasa,” yana mai cewa babu wani daga cikin iyalan Ganduje ko Gwamnatin Jihar Kano da yake da hannu a cikin mallaka ko shugabancin kamfanin.

“Zarge-zargen da ke cewa iyalan Ganduje suna cikin masu hannun jari ko shugabanni a Dala Inland Dry Port karya ce gaba ɗaya,” in ji Sanda. “Binciken da aka tabbatar daga Hukumar Rajistar Kamfanoni (CAC) da kuma takardun hukumar ya nuna babu wani daga cikin iyalan Ganduje da ya taɓa kasancewa mai hannun jari, darakta ko mai sanya hannu a harkokin kamfanin.”

Barr. Sanda ya bayyana cewa, asalin mallakar kamfanin na hannun wani ɗan kasuwa mai suna Ahmad Rabi’u, kafin City Green Enterprises (CGE) ta sayi kaso 80 cikin 100 na hannun jarin kamfanin, ta bar Rabi’u da kaso 20 cikin 100. Wannan cinikayya, a cewar sa, ta kasance karkashin tsarin doka kuma an tabbatar da ita a Hukumar CAC ba tare da wani hannun iyalan Ganduje ko gwamnatin Kano ba.

Dangane da rahotannin da ke cewa an bai wa ’ya’yan Ganduje hannun jari miliyan biyar kowannensu ta hanyar “ordinary resolution”, kamfanin ya bayyana wannan takarda a matsayin ta jabu da aka ƙirƙira domin haifar da rikicin siyasa.

“Wannan takardar ‘resolution’ ƙarya ce da wasu ke amfani da ita wajen neman lalata sunan wasu da kuma jawo rudani cikin harkar kamfani,” in ji Sanda.

Kamfanin ya kuma bayyana cewa gwamnatin Jihar Kano bata da kaso 20 cikin 100 a DIDP, inda ya bayyana cewa haɗin gwiwar da aka yi tsakaninsu kawai ta ta’allaka ne da taimakon ci gaban jama’a (CSR) wanda Hukumar Nigerian Shippers’ Council (NSC) ta jagoranta.

“Gwamnati ta bayar da tallafi wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa a wurin aikin Dala Dry Port domin bunƙasa tattalin arzikin Kano, amma wannan bai nufin mallakar kamfani ba,” in ji sanarwar.

Haka kuma, DIDP ta karyata zargin cewa wani jami’in gwamnati mai suna Abdullahi Haruna yana wakiltar jihar Kano a hukumar kamfanin. “Babu irin wannan mutum a cikin mu’amalolin kamfanin tun daga farko,” in ji sanarwar.

Kamfanin ya sake nanatawa cewa babu wani lokaci da iyalan Ganduje ko gwamnatin Kano suka kasance a matsayin masu hannun jari ko shugabanni, yana mai cewa duk takardun da aka gabatar a CAC tun kafuwar kamfanin har yanzu sun tabbatar da hakan.

“Ba za ka iya cire wanda bai taɓa kasancewa ɗan hannun jari ko darakta ba,” in ji sanarwar, yana mai bayyana rahotannin a matsayin wani yunƙuri na siyasa don ɓata suna da rage amincewar jama’a ga aikin tashar jirgin ƙasa ta cikin gida.

Kamfanin Dala Inland Dry Port na ɗaya daga cikin manyan ayyukan kasuwanci da sufuri a Arewacin Najeriya, wanda aka ƙirƙira domin rage cunkoson tashoshin ruwa na Lagos tare da ƙara haɓaka harkokin kasuwanci a Kano da makwabtan jihohi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...

Kananan Hukumomin Tarauni Rogo da Doguwa sun zamo koma baya wajen yin rijistar Masu zabe a Kano

Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa yanzu kananan hukumomin...