Mataimakin shugaban majalaisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibrin zai rabawa mutane sama da 10,000 masu karamin karfi daga kananan hukumomi 44 na Jihar Kano tallafin Naira 20,000 kowannensu .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa mataimakin shugaban Majalisar dattawan Nigeria shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, wanda ya bayyana cewa, za a fara tantance waɗanda za su ci gajiyar tallafin ne a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025, ta hanyar rarraba fom.
An bayyana cewa wannan shirin na bayar da tallafin kuɗi za a gudanar ƙarƙashin Gidauniyar Barau I Jibrin Foundation, wadda Sanata Barau ya kafa domin tallafawa al’umma. Gidauniyar ta gudanar da shirye-shirye da dama ciki har da bayar da tallafin karatun digiri na biyu a ƙasashen waje ga ɗaliban Kano.
Ismail Mudashir ya ce, wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin Sanata Barau domin taimaka wa marasa galihu da kai tallafi kai tsaye ga jama’ar jiharsa.
A cewarsa, “Mutane 6,500 za a zaɓa daga yankin Kano ta Arewa, inda kowace ƙaramar hukuma 13 za ta fitar da mutane 500. Sauran kuma, mutum 112 za a zaɓosu daga kowace ƙaramar hukuma a yankunan Kano ta Tsakiya da Kano ta Kudu.
Mudashir ya ƙara da cewa, “Ƙarfafa mata da matasa na daga cikin ginshiƙan ayyukan Sanata Barau domin haɓaka ci gaba a Arewa da ƙasar baki ɗaya.”