Bayan kwarmaton Danbello Gwamnatin Kano ta amince da kashe Naira biliyan 5.4 don gyaran makarantar Day Science da wasu makarantu

Date:

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da kashe jimillar kudin da ya kai Naira biliyan 5.397 domin gyaran makarantar Government Day Science College da sauran makarantun gwamnati a fadin jihar.

DAILY NIGERIAN ta tuna cewa ‘yan watanni da suka gabata, wani sanannen mai tasiri a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna mummunan halin da makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnati ke ciki.

A rana ta gaba bayan ya wallafa bidiyon, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar duba makarantar da kuma Government Technical College (GTC), inda ya bayar da umarnin a fara gyaransu nan take.

Sai dai, a zaman majalisar zartarwa ta 32 da aka gudanar a ranar 4 ga Oktoba, gwamnatin jihar ta amince da kashe Naira miliyan 905 domin cikakken gyaran makarantar, wadda aka kafa tun a shekarar 1993 a lokacin mulkin soja.

Sauran ayyukan da aka amince dasu sun haɗa da Naira miliyan 397 domin gyaran gine-gine a GSS Rimi, da ke karamar hukumar Sumaila.

Haka kuma, majalisar ta amince da kashe Naira biliyan 1.4 domin gyaran Government Technical College Kofar Nassarawa (GTC Kano).

Bugu da ƙari, ta kuma amince da Naira miliyan 546 don gyaran kwalejin noma ta Audu Bako da ke karamar hukumar Dambatta.

Majalisar ta kuma amince da Naira biliyan 1.8 domin gyaran ajujuwa da samar da kayan aiki i a makarantun firamare a fadin kananan hukumomi 44 na jihar, karkashin shirin CRC.

Sannan kuma, Naira miliyan 349 an amince da su domin gyaran gine-ginen makarantar SAS da ke karamar hukumar Birnin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...