Majalisar Wakilai Na Dubu Yiwuwar Gudanar Da Zaben Shugaban Ƙasa, Gwamnoni Da Na Yan Majalisu A Rana Ɗaya

Date:


‎Majalisar wakilai ta wakilai ta ce  ta na duba yiwuwar gudanar da zaben shugaban ƙasa, gwamna da kuma na majalisun dokoki a rana ɗaya, a wani yunkuri na sauya tsarin zabe a ƙasar nan.

‎Shugaban majalisar, Hon. Tajudeen Abbas, ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi tawagar wakilai daga Tarayyar Turai (EU) a Abuja, inda ya ce matakin zai inganta sahihancin zabe, rage kashe kudade, da kuma ƙara yawan masu kada kuri’a a gaba.


‎Abbas ya ce gudanar da dukkan zabe a rana guda maimakon yin su a ranaku daban-daban kamar yadda ake yi a yanzu, zai taimaka wajen kawar da ƙalubalen tsaro da matsalar rashin fitowar masu zabe.

‎Masu goyon bayan wannan kudiri sun bayyana cewa zai rage kashe kudade da rage hayaniya ta siyasa, ƙara yawan masu kada kuri’a da kuma rage matsalolin tsaro da ake fuskanta a lokutan zabubbuka.


‎Haka zalika, shugaban majalisar ya bayyana cewa akwai wasu sauye-sauyen da ake son a kundin tsarin mulki, ciki har da samar da kujeru na musamman ga mata da masu buƙata ta musamman, bayar da ’yancin kuɗi ga sarakunan gargajiya tare da fayyace rawar da za su taka, da kuma batun gudanar da dukkan manyan zabuka a rana guda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da...

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...