Nigeria@65: Muhimman Gabobi a jawabin Tinubu

Date:

‎Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa kasar ta shiga sabon salo na gyaran tattalin arziki, kuma matsin da ake ciki na dab da wucewa su zama tarihi.

‎A cikin jawabinsa ga ’yan kasa don bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai, shugaban ya ce gwamnatinsa ta damu da radadin da mutane ke ciki sakamakon gyare-gyaren da ake aiwatarwa.

‎Sai dai ya jaddada cewa da Najeriya ba ta dauki matakan da ta dauka ba, da tuni ta shiga halin karyewar tattalin arziki.


‎Tinubu ya tuna da jaruman da suka kafa kasar, yana mai cewa sun yi imani da cewa Najeriya ce jagorantar bakaken fata a duniya, kasancewar ita ce kasa mafi yawan jama’a bakaken fata.

‎Ya ce, “Ko da ba mu cimma duk burin da kakanninmu suka yi ba, amma ba mu kauce daga kan layinsu ba. A cikin shekaru 65 da suka gabata, Najeriya ta samu ci gaba mai yawa a fannin bunkasar tattalin arziki, hadin kan al’umma da ci gaban kasa.

‎”Yayin da sauki ya fi ga masu suka su dinga fadin abin da ya kamata, dole ne mu gane mu kuma yi murna da ci gaban da muka samu. A yau, ’yan Najeriya na da damar samun ilimi da kiwon lafiya fiye da a shekarar 1960,” ,” in ji shi.

‎Daukar matakai masu tsauri
‎Tinubu ya ce lokacin da ya hau mulki, ya gaji tattalin arzikin da ya kusa durkushewa sakamakon kuskuren manufofin kudi da rashin daidaito na tsawon shekaru.

‎Ya ce: “Mun fuskanci zabin da ya kasance mai sauki: ci gaba da tafiya da yadda ake yi ko kuma mu dauki hanyar gyara mai tsanani. Mun zabi hanyar gyara. Mun zabi gobe fiye da jin dadin yau.”


‎Shugaban ya ce kasa da shekaru uku bayan daukar wadannan matakai masu wahala, an fara ganin amfaninsu.

‎Ya ce gwamnatinsa ta kawo karshen tallafin man fetur da kumatsarin musayar kudade da mutane ’yan kalilan ke cin moriyarsa, yawancin al’umma ba sa amfana.

‎Mun karkata tattalin arzikin zuwa hanyar da kowa zai amfana, inda kudade ke tafiya zuwa fannin ilimi, kiwon lafiya, tsaro, noma da muhimman ababen more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki, intanet da ayyukan tallafi.

‎“Sakamakon wadannan matakai, yanzu gwamnati ta samu karin kudade a matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomi don kula da al’umma da warware matsalolin ci gaba.”

‎Ci gaban da aka samu

‎Tinubu ya ce gwamnatinsa na kokarin gina sabbin hanyoyi, gyara tsofaffi, da kuma gina makarantu da asibitoci.

‎Ya ce: “Ba mu da isasshiyar wutar lantarki don masana’antu da gidaje, ko kudaden gyaran hanyoyin da suka lalace, ko gina tashoshin jiragen ruwa, layin dogo da filayen jiragen sama masu inganci, saboda rashin zuba jari da ya kamata tun shekaru da suka wuce.”

‎Sai dai ya ce gwamnatinsa na gyara abubuwa:


‎“Ina farin cikin sanar da ku cewa mun wuce tsanani. Wahalhalun jiya sun fara sauyawa zuwa sauki. Ina murna da juriya da goyon baya da fahimtar da kuka nuna. Zan ci gaba da aiki domin ku, kuma ina sane da amincewar da kuka ba ni.

‎Tattalin arzikinmu na farfadowa da sauri. GDP na zango na biyu na 2025 ya karu da kaso 4.23 cikin 100, mafi sauri cikin shekaru hudu, ya zarce hasashen IMF na kaso 3.4 cikin 100. Hauhawar farashi ta sauka zuwa kaso 20.12 cikin 100 a watan Agusta 2025, mafi kankanta cikin shekaru uku,” in ji Tinubu.

‎Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa na kokarin bunkasa noma da tabbatar da wadatar abinci don rage farashin kayan masarufi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da...

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...