Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ta gaggauta sauya kwamishinan ‘yan sanda na jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda kwamishinan ya janye jami’an tsaro daga filin wasa na Sani Abacha lokacin taron.
Ya ce wannan mataki bai dace ba, kuma ka iya barazana ga tsaro da zaman lafiya a lokacin da ake gudanar da muhimmin bikin a kasa.
Idan za a iya tunawa dangantaka tsakanin gwamnatin Kano da Rundunar Yan sanda ta Kasa reshen jihar Kano ta yi tsami sakamakon zargin da gwamnan ya yi na cewa yan sandan ba sa bin umarninsa tun daga lokacin da ya Zama gwamna a shekarar 2023