Kungiyar Ma’aikatan Radio da Talbijin da Raya Al’adu ta Kasa reshen Jahar Kano (RATTAWU ) ta aike da sakon taya murna ga tsohon Shugaban kungiyar na jiha Comrade Muhammad Musa Muhammad Nya bisa nadin da akai masa a matsayin Sabon Shugaban gidan Radiyo da Talbijin din Hikima dake nan Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa ta taya murna da Shugaban kungiyar Comrade Babangida Mamuda Biyamusu ya aikowa Jaridar Kadaura24 a Kano.
Sanarwar ta bayyana nadin da cewa ya dace bisa La’akari da kwarewar sa a fanni yada labarai na tsawon shekaru.
Sanarwar ta bukaci ma’aikatan gidan su bashi cikakken hadin Kai da goyon baya domin samun Nasara. Sanarwar tayi addu’ar Allah yayi masa jagora yayin shugabancin sa.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a ranar litinin aka sanar da nada Muhammad Musa Inya a matsayin Sabon Shugaban gidan Radiyo da Talabijin na Hikima dake Kano .