Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke bikin fareti na ranar tunawa da samun ’yancin kai wanda aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, domin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai.
Wata sanarwa da Daraktan Sashen yada labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen, ya fitar ta bayyana cewa soke bikin fareti bai rage muhimmancin wannan babban tarihi ba, domin gwamnati ta jajirce wajen murnar cika shekaru 65 da samun ’yancin kai da mutunci da kuma kwazo.
Sanarwar ta ƙara da cewa, duk sauran shirye-shiryen da aka tanada domin bikin ranar ’yancin kai za su gudana kamar yadda aka tsara.
Haka kuma, gwamnati ta yaba da fahimta, goyon baya da haɗin kan ’yan Najeriya baki ɗaya, mambobin ƙungiyoyin diflomasiyya da kuma baƙi na musamman. Ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da mara wa gyare-gyaren Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin gina ƙasa mai ɗaukaka, in ji sanarwar.