Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatin da ta gaje shi Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu kudaden shiga da tallafin da suka fi yawa a cikin watanni shida kacal, idan aka kwatanta da abin da ya samu a duk tsawon shekaru 8 da ya shafe yana mulkin jihar.
Ganduje ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa, inda ya ce yana da tabbacin cewa duk da yawan kudaden da ake samu yanzu, ana bukatar a duba yadda ake kashe kudaden domin amfanin al’umma.
Ya kara da cewa: “Idan na kwatanta abin da muka samu lokacinmu da irin yadda ake samun kuɗi yanzu, sai dai akwai bukatar gwamnati ta yi wa jama’a cikakken bayani kan yadda ake amfani da wadannan kudaden.”
Wannan furucin na Ganduje na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta tattaunawa kan yadda ake amfani da kuɗaɗen shigar jihar Kano da gwamnatin yanzu ke karɓa.