Gwamnan Kano ya tura sunayen mutane biyu majalisar dokokin don nada su a mukaman Kwamishinoni

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen mutane biyu zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni kuma ya majalisar zartarwa ta jiha.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan kani, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadaura24.

Wadanda aka mika sunayensu sun hada da

1. Barista Abdulkarim Kabir Maude (SAN designate) – daga karamar hukumar Minjibir, mai shekara 40.

Ana sa ran Maude zai karɓi kambun matsayin lauya mafi kololuwa wato (SAN) a gaban kotun koli gobe litinin.

Ya kammala karatun lauya a jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, sannan ya samu digiri na biyu a fannoni biyu: International Economic Law daga Maryam Abacha American University of Niger da Business Commercial Law daga Jami’ar Bayero Kano.

Barista Maude ya shafe sama da shekaru goma yana aiki a fannoni daban-daban na lauya, ciki har da shari’a, harkokin kasuwanci, da kula da kadarori.

Shi memba ne na Kungiyar lauyoyin Najeriya wato Nigerian Bar Association da kuma Chartered Institute of Arbitrators of Nigeria.

2. Dr. Aliyu Isa Aliyu – Mai Shirin zama Farfesa a fannin lissafi, mai shekara 41.

Ya samu digiri na farko a Jami’ar Bayero Kano, Masters a Jordan University of Science and Technology, sannan ya yi Ph.D. a Firat University, Turkiyya.

Dr. Aliyu ya fara koyarwa a Jami’ar Tarayya Dutse a 2014, daga bisani ya zama Associate Professor a North West University, Kano. Ya kuma yi horo a kasashen China da Cyprus. Tun 2023, yana rike da mukamin Babban Mai Kidayar Jama’a/Kakakin Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano.

Shi ne ɗaya daga cikin masu cin gajiyar tallafin karatun waje na Kwankwasiyya, kuma ya taba rike mukamin sakataren kudi na jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano.

A wani bangare kuma sanarwar, ta ce Gwamna Yusuf ya amince da nadin Barista Salisu Muhammad Tahir a matsayin sabon Solicitor-General da Babban Sakatare na Ma’aikatar Shari’a ta Jiha.

Kafin nadin, Barista Tahir ya kasance Daraktan mai shigar da kara wato Public Prosecution a ma’aikatar, inda ya yi fice wajen gudanar da aikinsa.

An umarci shugaban ma’aikata da ya tabbatar da kammala dukkan matakan gudanarwa domin sabon Lauyan Gwamnatin ya fara aiki daga Litinin, 29 ga Satumba, 2025.

Gwamna Yusuf ya jaddada kudirinsa na ci gaba da zabar matasa masu kwarewa da gaskiya domin kara inganta aikin gwamnati a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...

NLC Reshen Kebbi Ta Soki Cire Naira Miliyan 14 Daga Albashin Malamai

Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Kebbi, ta...

Ziyarar Aiki: Shugaba Tinubu Ya Iso Lagos

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya isa birnin Lagos...