Ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowace ƙasa, kuma cibiyoyin ilimi masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen faɗaɗa damar samun guraban karatu a Afirka. Daga cikin irin waɗannan cibiyoyi akwai Maryam Abacha Group of Universities (MAAUN), wacce ta zama wani muhimmin ginshiƙi na gina ƙwarewar yan Adam. An kafa makarantar domin samar da ingantaccen ilimi kuma cikin sauƙi da rahusa, kuma wanda za a za a iya gogayya da shi a duniya. Yanzu haka an kafa jami’o’in Maryam Abacha a Najeriya da kasashen ƙetare, domin bai wa dubban ɗalibai damar samun ingantaccen ilimi.
Faɗaɗa Damarmakin Samun Ilimi
Ɗaya daga cikin manyan gudunmawar MAAUN ita ce faɗaɗa damar shiga jami’a ga ɗalibai. A ƙasashen Afirka da dama, ana fustantar ƙarancin guraben shiga jami’o’in gwamnati, wanda hakan na hana dubban daliban da suka cancanci damar ci gaba da karatu. Tuni MAAUN ta cike wannan gibin kamar haka:
Bai wa dubban ɗalibai guraben shiga jami’a.
Samar da fannoni daban-daban kamar likitanci, lauya, kimiyyar zamantakewa, kasuwanci da fasaha.
Bada damar karatu ga ɗalibai daga ƙasashen waje.
Gudunmawa Wajen Gina Ɗan Adam
Jami’o’in MAAUN sun taka muhimmiyar rawa wajen bai wa matasa ilimi da ƙwarewar da za su taimaka wajen ci gaban ƙasa. Misali:
Fannin Lafiya: Sun shahara wajen samar da likitoci, malamin jinya, da masu harhada magunguna waɗanda ke aiki a asibitoci da cibiyoyin lafiya a faɗin Afirka.
Kasuwanci da Ƙirƙira: MAAUN ta na mai da hankali wajen koyar da sana’o’in kasuwanci don ɗalibai su zama masu samar da aikin yi ba masu neman aiki kawai ba.
Samar da Ƙwararru: Ana tsara darussa a jami’ar daidai da yadda ake yi ko’ina a duniya domin tabbatar da cewa ɗaliban MAAUN na iya gogayya da takwarorinsu na duniya.
Huldar Ilimi Da Kasashen Ƙetare
MAAUN na taka muhimmiyar rawa wajen yin hulda da kasashen ketare Kan abun da ya shafi harkar ilimi kamar haka:
Dakunan Kwanan Ɗaliban jami’ar suna kafada da kafada da na jami’o’in kasashen Turai, Asiya da Amurka.
Ɗalibai na samun damar yin mu’amalar karatun da takwarorinsu na sauran kasashe .
Ana amfani da harshen Turanci wajen koyarwa wanda yake sauƙaƙa Ɗaliban wajen mu’amalar ta yau da kullum a duniya.

Bunkasa Tattalin Arzikin Al’umma
MAAUN ta bunkasa tattalin arzikin al’ummomin da suke kewaye da jami’ar.
Ƙirƙirar Ayyukan Yi: Dubban al’ummar yankin sun sami aikin malunta da sauran aiyuka a jami’o’in.
Ci gaban Garuruwa: Gina jami’o’i ya jawo sababbin kasuwanci, ya ƙara buƙatar gidaje, kuma ya motsa tattalin arzikin yankunan.
Ayyukan Jama’a: Akwai shirye-shiryen kiwon lafiya, bincike, da ayyukan al’umma da makarantar ke gudanarwa don taimakon jama’a.
Ƙara Darajar Najeriya A Fagen Ilimi
MAAUN ta ƙara wa Najeriya suna a matsayin cibiyar ilimi a Afirka. Tana jawo ɗalibai daga ƙasashen daban-daban, wanda hakan ke ƙarfafa haɗin kan Afirka a fannin ilimi tare da bunƙasa ɗaukaka Najeriya a idon duniya.
Kammalawa
Jami’o’in Maryam Abacha sun zama ginshiƙin ci gaban ilimi a Afirka. Ta hanyar buɗe ƙofofin ilimi, ƙarfafa haɗin kan ƙasa da ƙasa, da kuma saka hannun jari a fannoni masu muhimmanci kamar lafiya, Ilimin aikin lauya da kasuwanci, sun taɓa rayukan dubban mutane. Ba kawai fannin ilimi ba, tasirinsu ya wanzu a fannin ayyukan yi, kiwon lafiya da tallafa wa al’umma. Domin dorewar wannan gagarumar gudunmawa, ana buƙatar ci gaba da saka hannun jari a ingancin ilimi, bincike da ƙirƙira.