‎Yada labaran karya a intanet babban laifi ne a Musulunci – Sheikh Ibrahim Khalil

Date:


‎Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya gargadi masu yada labaran karya musamman a kafafen sada zumunta da su daina, domin Musulunci ya haramta hakan.

‎Ya bayyana cewa a Musulunci, yada labaran karya daidai yake da yin karya, kuma addinin Musulunci yana tsananin kin masu karya.

‎Sheikh Khalil ya fadi hakan ne a Kano a ranar Talata yayin wani taron horaswa na kwanaki biyu da aka shirya wa malamai da limamai kan yadda za a yaki labaran karya da kuma inganta fahimtar kafofin yada labarai, wanda kungiyar Alkalanci ta shirya, wata kungiya da ke tantance gaskiyar labarai da ilmantar da jama’a.


‎A cewar malamin, “Musulunci ya riga ya haramta yin karya, kamar yadda Allah ya gargade mu a cikin Alkur’ani: ‘Kada ku bi abin da ba ku da ilimi a kansa. Hakika kunne, ido da zuciya, duk abubuwan tambaya ne a gare ku’.

‎“Saboda haka, kirkira da yada labaran karya ba su da bambanci da yin karya, wanda laifi ne,” in ji shi.

‎Ya kara da cewa malamai na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen ilmantar da jama’a game da hadarin yada labaran karya, musamman a intanet da kafafen sada zumunta.


‎Tun da farko da yake jawabin maraba, Editan Alkalanci kuma wanda ya shirya taron, Alhassan Bala, ya jaddada muhimmancin shirya bitar ga malaman.

‎“Muna rayuwa a wani zamani da bayanai ke yaduwa cikin sauri fiye da da. Abin takaici, yawancin abin da ake yadawa yana da rudani, raba kan jama’a, kuma yana da illa,” in ji shi.


‎Bala ya bayyana cewa an tsara taron musamman don malamai saboda tasirinsu a cikin al’umma.

‎“Wa’azinku da koyarwarku suna da tasiri wajen gina ra’ayin jama’a. Tare da wannan amana, akwai nauyin tabbatar da cewa abin da kuke yadawa gaskiya ne, an tabbatar da shi, kuma yana da amfani,” kamar yadda ya fada wa mahalarta bitar.


‎Ya ce tun bayan kafuwarta a watan Oktoban bara, kungiyar Alkalanci ta mayar da hankali kan yaki da labaran karya da ake yadawa da Hausa, tare da niyyar fadada ayyukanta a fadin Najeriya.

‎Ya jaddada cewa har manyan shugabanni da ake girmamawa na iya yada karya ba tare da sun sani ba, lamarin da ke nuna muhimmancin tunani mai zurfi da tabbatar da gaskiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...

Gwamnan Kano ya tura sunayen mutane biyu majalisar dokokin don nada su a mukaman Kwamishinoni

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika...

NLC Reshen Kebbi Ta Soki Cire Naira Miliyan 14 Daga Albashin Malamai

Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Kebbi, ta...