Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Date:

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila, OFR, PhD, ya bayyana farin cikinsa kan matakin da gwamnatin Kano ta dauka na mikawa majalisar dokokin jihar kudirin doka da zai baiwa kananan hukumomi 44 na jihar cikakken ikon kudi da na gudanarwa. Ya bayyana wannan mataki a matsayin shaida da kuma sakamako na gwagwarmayar da ya fara a matakin kasa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimaki na musamman ga sanata Kawu Kan harkokin yada labarai Abbas Adam Abbas ya aikewa manema labarai.

Idan za a iya tunawa dai Jaridar Kadaura24 ta rawaito Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da kudirin doka a yayin zaman majalisar zartarwa karo na 31 da aka gudanar a ranar alhamis, 11 ga Satumba 2025.

Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, inda ya bayyana cewa kudirin yanzu zai tafi majalisar dokokin jihar domin tattaunawa da amincewa.

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Haka zalika, A ranar 15 ga Mayu 2024, Sanata Kawu ya gabatar da wani kudiri a majalisar dattawan Najeriya, inda ya nemi dawo da ikon kananan hukumomi. Wannan mataki daga baya ya samu karfi bayan nasarar da aka samu a kotu karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya tabbatar da cin gashin kai ga dukkan kananan hukumomi a kasar.

Da yake mayar da martani kan wannan sabon ci gaba a Kano, Sanata Kawu ya ce hakan ya tabbatar da gaskiyar matsayinsa na cewa cin gashin kananan hukumomi na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da dimokuradiyya, ci gaban al’umma da kuma gaskiya a tafiyar da shugabanci.

FB IMG 1753738820016
Talla

“Wannan nasara ce ga dimokuradiyya da al’ummar Najeriya. Abin da aka fara a zauren majalisar dattawa, aka kuma kare a kotu, yanzu ya zama gaskiya a matakin jiha. Ina jin dadi ganin Jihar Kano ta rungumi cikakken tsarin cin gashin kai na kananan hukumomi,” in ji Sanata Kawu.

Ya kara jaddada aniyarsa ta ci gaba da fafutukar kawo sauye-sauye a dimokuradiyya da za su baiwa ‘yan kasa damar shigowa cikin mulki tare da karfafa shugabanci a fadin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...

Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta haramta auren jinsi

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta...

Yan sanda a Kano sun lashi takobin samar da ingantaccen tsaro a ranar Takutaha

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori,...