Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ta amince da kashe naira biliyan 18.8 domin aiwatar da ayyuka fiye da 30 a fannonin ilimi, kiwon lafiya, muhalli da samar da hanyoyi.
Amincewar ta fito ne daga taron majalisar karo na 31 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano dake Kwankwasiyya City.
Daga cikin ayyukan akwai gina sabbin hanyoyi da magudanan ruwa, gyaran makarantu da suka kone, da wasu manyan makarantun gwamnati, da kuma rarraba kayayyakin makaranta ga ɗaliban firamare a shekarar 2025/2026.
Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta haramta auren jinsi
Haka kuma, an ware kudade don gina sabon asibitin gidan gwamnati, gyaran makarantar kiwon kaji a Dambatta, da samar da rijiyoyin burtsatse 14 masu amfani da hasken rana.
Majalisar ta kuma amince da samar da fitilun tituna masu amfani da hasken rana a kananan hukumomi da dama ciki har da Bagwai, Dawakin Kudu, Ghari, Kabo, Minjibir da Shanono.

Kazalika, an tura kudurori biyu zuwa majalisar dokokin jihar domin aiwatar da hukuncin kotun koli kan ikon kananan hukumomi, abin da gwamnatin ta ce zai tabbatar da gaskiya, adalci da ci gaban al’umma.