Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta ƙasa reshen Kano dake tashar Kofar Wambai ta roƙi Gwamnatin Jihar Kano da ta kafa kwamitin kar-ta-kwana domin sa ido kan tashoshin mota da ke ɗaukar fasinjoji ba bisa ƙa’ida ba.
Shugaban ƙungiyar tashar motoci ta Kofar Wambai, Alhaji Salisu Sani Yau Gareka, ne ya yi wannan kira a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin ƙungiyar dake cikin tashar.
Alhaji Salisu ya ce ɗaukar fasinjoji a bakin titi na kawo cikas ga ci gaban harkar sufuri a jihar Kano, lamarin da ya ce ya daɗe yana damun masu sana’ar.
“Akwai buƙatar Gwamnati ta ɗauki matakan da za su kawo ƙarshen wannan matsala wadda ta jima tana hana harkar sufuri ta bunƙasa kamar yadda ya kamata, kamar yadda ake gani a wasu jihohi.” a cewasa
Rijistar Zabe: Gidan Rediyon Kano Ya Ƙara Zage Dantse Wajen Wayar da Kai Kan Al’umma
Ya ƙara da cewa ƙungiyar tashar Kofar Wambai za ta ci gaba da mara wa Gwamnatin Jihar Kano baya a duk wani shiri da zai kawo cigaban harkokin sufuri.
Shugaban ƙungiyar ya yi nuni da cewa kamar yadda Kano ta yi suna a harkar kasuwanci, za ta iya samun gagarumar nasara a fannin sufuri idan aka samu tsari na gaskiya da bin dokoki.

Haka kuma, ya shawarci direbobin haya a jihar Kano da su riƙa bin ƙa’idar shiga tashoshin mota don kaucewa asarar kudaden shiga na gwamnati, domin waɗannan kuɗaɗen su ne ke taimaka mata wajen gudanar da ayyukan raya jiha.
Daga ƙarshe, Alhaji Salisu ya tabbatar da cewa ƙungiyar tashar Kofar Wambai za ta ci gaba da goyon bayan manufofin gwamnati, musamman wajen samar wa matasa ayyukan yi don rage shaye-shaye, sata da sauran munanan dabi’u. Ya kuma yi kira ga mambobin ƙungiyar da su ƙara ɗaurewa wajen mara wa ƙungiyar baya domin ci gaban al’umma baki ɗaya.