Yadda Abdulmumin Kofa ya so ya yi dillancin yan Kwankwasiyya a wajen Tinubu – Hadimin Gwamnan kano

Date:

Ra’ayin Salisu Yahaya Hotoro

Salisu Yahaya Hotoro shi ne Babban Mai taimakawa gwamnan jihar Kano Kan harkokin soshiyar media na daya kuma yana daga cikin Makarantar gwamnan cikin manyan Masu taimakawa gwamnan.

Idan za’a iya tunawa a jiya Asabar Kadaura24 ta rawaito cewa jam’iyyar NNPP ta bakin shugabanta na jihar Kano Hashim Sulaiman Dungurawa ya bayyana cewa sun kori Dan Majalisar Mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji daga jam’iyyar saboda dalilai na zargin yiwa jam’iyyar zargon Kasa da kin biyan wasu hakkoki na jam’iyyar.

Sai dai daga bisani Kadaura24 ta kawo Rahoton cewa Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce ya karbi korar da aka yi masa , harma ya yi alkawarin biyan kudin da aka ce jam’iyya tana binsa.

Hakan tasa Salisu Yahaya Hotoro ya wallafa wani rubutu a sahihin shafinsa na Facebook inda ya zargi Kofa da kokarin yin dillancin yan Kwankwasiyya a wajen shugaban Kasa Tinubu .

Ga yadda rubutun nasa ya kasance:

A TAƘAICE: Shi Audu Kofa so yayi ya zama dillalin cefanar da Jagora, Gwamna da ilahirin Ƴan Kwankwasiyya a wajen shugaban ƙasa daga ƙarshe idan ciniki ya faɗa sai a bashi kujerar minista a matsayin la’adar dillacinsa.

Bayan ficewa daga NNPP Abdulmumin Jibrin Kofa ya kalubalancin matakin korarsa

Ita kuma jam’iyyar NNPP sai take ganin ai ko da akwai wani mutum a duniya ko wasu mutane daya kamata ace sunyi dillacin Ƴan Kwankwasiyya a wani waje bai kamata ace sun wuce Jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ko Gwamna Alhaji Abba K Yusuf ba domin kuwa sune suka fi kowa dacewar su jagorance a kowacce irin tafiya ba mutumin dake kwadayin iya la’adar da zai samu ba.

Cikin mutuntawa jam’iyya ta kira Audu Kofa ta gaya masa cewa ya tsaya ya nutsu ya bar duk wata rawar ƙafa da sunan zama dillalin da ba’a bashi tallan kaya ba, aka fito ɓaro-ɓaro aka gaya masa cewar duk wanda yake son ƙulla wata alaƙar siyasa da Ƴan Kwankwasiyya to kai tsaye Jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ko Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf sune mutanen da zai zauna da su a matsayin wakilai ya tattauna da su ba wani mutum ba.

Da Audu Kofa ya fahimci gargadin da akayi masa sai ya ruga gidan TV na Channel yana sambatu ciki hadda tallata Ɗan jam’iyyar da ba nasa ba.

FB IMG 1753738820016
Talla

Ita kuma jam’iyyar NNPP jam’iyya ce mai tsari da bin dokoki ba irin jam’iyyar PDP bace da wani zai zame mata karfen ƙafa har a bashi kwamishina a gwamnatin Ganduje ko a bashi minista a gwamnatin Tinubu amma a rasa yadda za’a yi da shi, kai tsaye jam’iyya uwar kowa tayi waje rod da Audu Kofa.

Saboda haka yanzu za’a sake sabon lale, masu son hadaka da mu yanzu zasu gane cewar sun tsalleke mai kaya sun tafi suna tattaunawa ne da dillali bayan da mai kaya ya gano dillali yana kokarin cutarsa kuma yace ya kori wannan dillalin, saboda haka duk mai son tattauna wata magana da yan Kwankwasiyya to kai tsaye Jagora Kwankwaso ne abin nema ba wani a wani waje ba.

Ra’ayin Salisu Yahaya Hotoro Hadimin gwamnan Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...