Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa (Jarman Bebeji), ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.
A wata sanarwa da ya fitar, Kofa ya ce ya yi mamaki ganin yadda aka kore shi daga jam’iyyar ba tare da an ba shi damar kare kansa ba.
Ya bayyana cewa maganganun da ya yi a tattaunawar da ya yi da yan Jarida a ranar alhamis bai kamata su zama dalilin korar sa daga jam’iyyar ba, domin kuwa a cewarsa, hakan ya yi daidai da ka’idojin jam’iyyar da ke ba da damar bayyana ra’ayin kashin kai.
“Ba a gayyace ni in kare kaina ba, ko in yi bayani ga kowanne bangare na jam’iyya. Wannan ya sabawa adalci da mu ka dade muna kira a kansa. Ko a lokacin mulkin soja, ana bai wa wanda ake zargi damar kare kansa,” in ji shi.
Da dumi-dumi: NNPP ta kori Abdulmumin Jibrin Kofa daga jam’iyyar
Jibrin ya kara da cewa da yake yana girmama jam’iyyar, bai zai dauki matakin shari’a ba, duk da cewa a cewarsa, ba a bi ka’ida ba wajen korar sa . Ya ce ya karbi hukuncin jam’iyyar a matsayin kaddara kuma ba tare da jin haushi ba.
Game da zargin rashin biyan kudin mamba, Jibrin ya ce bai taba kin biyan kudin ba, yana mai rokon jam’iyyar ta turo masa da lissafi domin ya biya nan take. Ya yi kira ga jam’iyyar da kada ta dauki hanyar cin mutunci ko suka don tana son rabuwa da shi ba, yana mai cewa dangantaka zata ci gaba da kasancewa duk da bambancin jam’iyya.

Jibrin ya kuma nuna rashin jin dadi kan yadda jam’iyyar ke kallon cewa babu wani dan siyasa da ke da muhimmanci a cikinta, yana mai cewa: “Na gode wa Allah da duk wata daraja da na samu, zan fi son in kasance a Inda za a rika ganin daraja da mutuncina.”
A karshe, ya gode wa jam’iyyar bisa goyon bayan da ya samu a lokacin da yake cikinta, tare da bayyana cewa zai yi nazari kafin ya sanar da sabuwar jam’iyyar siyasa da zai koma.