Zargin Harbi: ‘Yan Sanda Sun Gayyaci Shugabar K/H Tudun Wada

Date:

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta gayyaci Hajiya Sa’adatu Salisu, shugabar ƙaramar hukumar Tudun Wada kuma shugabar ƙungiyar shugabannin kananan hukumomi (ALGON) a Kano, domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen kai hari ga ma’aikatan wata masana’anta.

Rahotanni sun bayyana cewa ta jagoranci wasu ‘yan daba fiye da 200 dauke da makamai, suka kai farmaki kan ma’aikata a masana’antar Tasarrufi General Enterprise. An ce a lokacin tashin hankalin, ta umarci dogarinta mace wacce ‘yar sanda ce ta buɗe wuta, lamarin da ya jawo raunin wani ma’aikaci a hannu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da cewa an gayyaci dukkan ɓangarorin da abin ya shafa – ciki har da shaidun gani-da-ido, wacce ake zargi, da kuma dogarinta – domin gudanar da bincike mai zurfi.

Ya ce rundunar za ta tabbatar da adalci tare da tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa doka.

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano ta Fitar da Kudin Ajiya da Adadin Kujerun Hajji na 2026

Guda Cikin Matasan Mustapha Bashir Tudun-Wada, wanda shi ma ya jikkata, ya shaida Kadaura24 cewa: “Muna zaune Muna aiki kawai muka ji mutane ne sun zo da Malamai suna dukan mu da Makaman har suka ji wa kusan mutane 7 daga cikin mu ciwo. Wannan abin da aka yi mana ba za mu yafe ba.”

Ya ce sun yi mamakin yadda aka zo aka far musu suna tsaka da gudanar da sana’arsu , Maimakon ita Shugabar karamar hukumar ta karfafesu amma sai ta buge da korarsu tare da sa yan daba su sassaresu.

Shi ma Ma’ud Tahir guda ne cikin wadanda suka jikkata ya ce ya cika da mamakin yadda shugabar Karamar Hukumar Tudun wada ta Jagoranci yan daba wajen Kai musu farmaki .

FB IMG 1753738820016
Talla

” An sare ni da adda kuma haka aka rika sararmu ni da abokan aikinna a lokacin da muke tsaka da aiki, bayan kuma a bayan ta rushe mana wajen sana’ar Amma har yanzu bata bar mu ba”.

Ya ce suna kira ga Gwamnan jihar Kano da hukumomin tsaro da su binciki Wannan lamari tare da daukar matakin da ya dace akan Shugabar karamar hukumar Tudun Wada Hajiya Sa’adatu Salisu don a tabbatar an yi musu adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...