Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja yau Alhamis, 4 ga Satumba, domin fara hutun shekara ta 2025 a Turai.
Sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai Mista Bayo Onanuga, ya fitar ta ce hutun zai ɗauki kwanaki 10 na aiki.
Shugaba Tinubu zai kwashe lokacin hutun nasa tsakanin ƙasashen Faransa da Birtaniya, kafin daga bisani ya dawo gida Najeriya.