Kungiyar ’Yan Jarida Mata ta Najeriya (NAWOJ) ta yi kira ga jama’ar Kano da ma fadin kasar nan da su yi tururuwa wajen yin rijistar zabe da ake ci gaba da gudanarwa.
Shugabar kungiyar ta kasa, Hajiya Aisha Ibrahim, ta bayyana haka a wani taro da ta yi da ’yan jarida a Kano, inda ta jaddada muhimmancin samun Katin Zabe na Dindindin (PVC) ga kowane dan kasa mai kishin kasa.
A cewarta, yin rijistar kuri’a da karbar PVC shi ne makamin da ’yan kasa za su yi amfani da shi wajen zabar shugabannin da za su tsara makomar jiharsu da kasar baki daya.
Al’umma Sun Zargi Shugabannin Babban Asibitin Rano Da Kwashe Kayan Aikin Asibitin
Hajiya Aisha ta kuma ce wannan kira na kungiyar ya yi daidai da na Kwamishinan Yada Labarai na Kano, Alhaji Abdullahi Waiya, wanda ya nemi jama’a da su ba wa batun rijistar muhimmanci.

Sakataren kungiyar na kasa, Wasilah Ladan, ta tabbatar da cewa NAWOJ za ta ci gaba da wayar da kan al’umma kan muhimmancin shiga harkokin dimokuradiyya domin ganin an samu dimokuradiyya mai wakilci da gaskiya.
Kungiyar ta yi imani cewa dimokuradiyya ba za ta yi tasiri ba sai idan al’umma suka yi rijista da kuma amfani da hakkinsu na kada kuri’a.