Al’umma Sun Zargi Shugabannin Babban Asibitin Rano Da Kwashe Kayan Aikin Asibitin

Date:

Al’ummar Karamar Hukumar Rano sun yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan Lafiya na jihar da su kawo musu dauki kan matsalar da ta shafi Babban Asibitin Rano, inda ake zargin an kwashe wasu muhimman kayan aikin lafiya.

Aliyu Harazimi Rano, wanda ya yi magana a madadin al’ummar yankin, ya ce sun wayi gari ba su kara ganin kayan aikin zamani da aka sanya domin kula da lafiyar jama’a ba. Ya yi zargin cewa shugabannin asibitin na da hannu wajen sayar da kayan ko kuma kwashe su zuwa wasu wurare.

A cewarsa, tun bayan shigar da wadannan kayayyaki a asibitin, jama’ar Rano sun daina zuwa Asibitin Murtala da sauran manyan asibitoci a Kano domin neman magani. Amma yanzu da kayan suka bace, al’ummar yankin za su sake fuskantar wahalhalu wajen samun lafiya.

“Kayayyakin da muke zargin an kwashe sun hada da babban injin Scanning, injinan kula da masu matsalar idanu da sauran muhimman kayan aiki. Hatta batir da sauran kayan aikin hasken solar da kamfanonin A.A Rano da Salbas suka samar, duk an kwashe su,” in ji shi.

Kwamitin Ganduje Kan Koran Jami’an Hisba A Kano Ya Fara Aiki

Ya roki gwamnatin jihar da ta gudanar da bincike kan lamarin domin kada a batawa gwamnatin Abba Kabir Yusuf suna. “Mun san Gwamna Abba ba zai bayar da umarnin a kwashe kayan ba, haka ma Kwamishinan Lafiya. Amma muna da zargin cewa shugabannin asibitin Rano ne ke da hannu, don haka muke kira ga gwamnati ta bincika wannan al’amari,” in ji shi.

FB IMG 1753738820016
Talla

Da aka tuntubi Hukumar Kula da Asibitoci ta Kano kan lamarin, Jami’ar Hulda da Jama’a ta hukumar, Samira Abdullah, ta shaida wa jaridar Kadaura24 cewa tuni shugaban hukumar ya kafa kwamiti domin binciken gaskiyar lamarin, kuma da zarar sun kammala binciken za su sanar da jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...