Zargin Almundahana: EFCC da ICPC Sun Gano Naira Biliyan 6.5 A Asusun Guda Cikin Manyan Hadiman Gwamnan Kano

Date:

 

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaka da hakan (ICPC) tare da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Satar Dukiyar Jama’a (EFCC) sun gano Naira biliyan 6.5 da ake zargin suna da alaka da Abdullahi Ibrahim Rogo, Darakta Janar na harkokin tafiye-tafiyen gwamnan jihar Kano.

A cewar wasu takardu da jaridar DAILY NIGERIAN ta samu, hukumomin yaki da cin hanci da rashawar sun zargi hadimin na Gwamna Abba Kabir Yusuf da karkatar da kudaden jihar ta hannun wakilai.

FB IMG 1753738820016
Talla

An ruwaito cewa wannan gagarumar satar ta dukiyar al’umma ta faru tsakanin shekarar 2024 zuwa Fabrairu 2025.

Takardun sun bayyana cewa Rogo ya yi amfani da kamfanonin H&M Nigeria Limited, A.Y. Maikifi Petroleum, da Ammas Oil and Gas Limited wajen karkatar da kudi daga ofishin sa zuwa ga abokan harkallar sa.

Binciken hukumomin ya nuna cewa kudaden an biya su ne a matsayin kwangiloli na bogi da ba a taba bayarwa ko aiwatarwa ba.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta gano cewa A.Y. Maikifi Petroleum Limited da Ammas Oil and Gas Limited sun karɓi naira biliyan 1.17 daga Asusun Kason Kudaden Gwamnatin Tarayya na Jihar Kano.

“A wasu lokuta daban-daban, an sa wadannan kamfanoni biyu su sanya hannu a kan takardun izini daga tsohon Akanta Janar na Jihar Kano, Abdulsalam Abdulkadir, inda ya baiwa ma’aikatar albarkatun ruwa ta jihar izini da ta tura N539,230,000.00 da N570,000,024.50 bi da bi, zuwa asusun kamfanonin canjin kudi guda biyu, Kazo Nazo Global Resources da Namu Naku Ne, a matsayin biyan kuɗin kwangilolin bogi.

“Daga nan sai aka canja kudaden zuwa dalar Amurka sannan aka mika su a tsabar kudi ga Abdullahi Ibrahim Rogo, ta hannun Nasiru Girma [Manajan Daraktan Kazo Nazo] da wani Ghali Muhammad [abokin kasuwancin Nasiru Girma], wanda ya hada Rogo da su.”

Takardun kotu da wannan jarida ta samu sun nuna cewa Rogo da wasu da aka ambata sun amsa laifinsu ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa.

Sai dai daga baya ya canja baki, har ya shigar da kara a babbar kotun jihar Kano, reshen Bichi, domin hana a kama shi ko a gurfanar da shi.

A cikin bayanan ƙarar da suka shigar, duka ICPC da EFCC sun bayyana cewa akwai shaidu karara da ke nuna cewa wadanda ake zargi sun aikata satar kudade.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...