Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi kiran samar da sauye-sauye a tsarin Majalisar Dinkin Duniya don bai wa Afirka kujerun dindindin biyu a kwamitin tsaro na Majalisar.
Yayin da yake jawabi a taron duniya kan ci gaban ƙasashen Afirka a birnin Yokohama na ƙasar Japan, Tinubu ya ce nahiyar Afirka ta cancanci matakin saboda irin gudunmowarta ga zaman lafiya.

“Babban burin Najeriya shi ne Afirka ta samu cikakken wakilci a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya,” in ji Tinubu.
Gwamna Abba ya rantsar da sabon shugaban hukumar hana cin hanci da rashawa ta Kano
Shugaban na Najeriya ya ce nahiyar na samun damar samun hawa kujerar na-ƙi, baya da ƙarin wakilci a kujerun da ba na dindindin ba.
Bola Tinubu ya kuma jinjina wa dakarun tsaron Najeriya kan nasaroroin da ya ce sun samu a baya-bayan nan kan yaƙi da ta’addanci a ƙasar.