Duk da umarnin kotu, APC ta bayyana Bangaren Shekarau a matsayin haramtacce

Date:

Daga Zara Jamil Isa
  Shugabancin jam’iyyar APC ta kasa ya bayyana wani bangare na jam’iyyar a jihar Kano karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau a matsayin haramtacce.
 Sakataren Kwamitin Tsare Tsare-Tsare na Jam’iyyar APC mai rikon kwarya, Sanata John James Akpanudoedehe, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a, babban birnin Abuja.
 Idan Zaku iya tunawa Kadaura24 ta rawaito wata babbar kotun Abuja ta amince da taron da bangaren Shekarau ya gudanar tare da soke na bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje.
 Alkalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu, a hukuncin da ya yanke ya hana bangaren Ganduje aina kansu a Matsayin Shugabanin jam’iyyar a Jihar Kano .
 Bangaren Ganduje ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban kungiyar, yayin da bangaren Shekarau ya zabi Haruna Ahmadu Danzago, a lokaci da aka gudanar a Zaben a  ranar 16 ga watan Oktoba.
 Da yake magana da manema labarai, Akpanudoedehe ya bayyana cewa zaben da bangaren Ganduje ya gudanar shi shugabannin jam’iyyar suka amince da su kuma shi ne akan ka’ida.
 Politics Digest ta rawaito John ya tabbatar da cewa jam’iyyar ba ta aika kwamitoci biyu don yin zabe kala biyua a jihar kano ba, yana mai bayyana mambobin da suka halarci taron da bangaren Shekarau ya gudanar a matsayin masu zagon kasa ga jam’iyyar.
 Sakataren jam’iyyar APC, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki ba ta samu ta yi nazarin hukuncin da kotu l ta tabbatar da bangaren Shekarau ba.
 “Mu ne shugabannin jam’iyyar Kuma mu mu ke da alhaki ba za mu so yin tsokaci kan hukuncin da ba mu gani ba.
 “Abin da zan iya gaya muku a yanzu shi ne, za mu nemi kwafin  hukuncin domin yin nazari akan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...