Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana godiya ga mutanen mazabar Bagwai da Shanono bisa goyon bayan da suka nuna wa jam’iyyar a zaɓen cike gurbi da aka kammala.
A wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, Kwankwaso ya bayyana nasarar ɗan takarar NNPP, Ali Lawan Alhassan, a matsayin babbar nasara, ya na mai cewa hakan ya nuna a fili inda amincin jama’a ya ke yanzu da nan gaba.

Ya kuma yabawa shugabanni da magoya bayan jam’iyyar bisa jajircewa da kuma gudanar da zaɓen cikin lumana da tsari na dimokuraɗiyya.
A Hukuma ce INEC ta bayyana sakamakon zabukan cike gurbi da aka yi a kano
“Mutanen Bagwai da Shanono sun yi magana a bayyane ta hanyar kada ƙuri’a mai tarin yawa ga jam’iyyar NNPP. Nasarar da Ali Lawan Alhassan ya samu a fili take cewa ga inda amincin jama’armu yake, yanzu da nan gaba,” in ji Kwankwaso.
Ya ƙara jinjinawa jajircewar ‘yan jam’iyyar da magoya baya da suka yi aiki tukuru domin tabbatar da gudanar da zaɓen cike gurbin cikin lumana da nasara.