PDP ta yi watsi da zaben cike gurbi na Bagwai da Shanono dake Kano

Date:

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta yi fatali da yadda aka samu wadanda suka kawo karantsaye a zaben cike gurbi a mazabun Shanono-Bagwai.

A sakon da ya gabatar ga manema labarai a wannan Asabar shugaban jam’iyyar ta PDP a Kano Yusuf Ado Kibiya, da kakkausar murya ya yi Allah wadarai da yadda aka samu tada hankula da tursasawa masu kada kuri’a abin da zai shafi makomar sakamakon zaben, yace abune da ba za a lamunta ba.

FB IMG 1753738820016
Talla

“Mun samu rahotanni na yin barazana da amfani da ‘yandaba matakin da ke zama zagon kasa ga tsarin dimukuradiyya.”

“Amfani da tashin hankali don tursasa masu zabe da ‘yantakara ko murda sakamakon zabe abu ne da ba za a lamunta ba, kuma da kakkausar murya dole mu yi Allah Wadarai da shi, irin wannan mataki ba kawai barazana ga rayuwar jama’a ba, zai rusa amincewa tsakanin al’umma da masu rike da madafun iko.”

Jam’iyyar APC ta bayyana matsayarta kan zaben cike gurbi a Kano

Yace rasuwar tsohon danmajalisar na yankin na Shanono-Bagwai ya samar da babban kalubale ga al’ummar da ke wannan yanki wadanda ke son ganin an masu adalci da samar da zaman lafiya akuma bi ka’idoji na doka.

“ Mun yi watsi da halayyar da wasu suka nuna wacce ke da muradi na murda harkokin zabe don cimma wata manufa ta wasu daidaikun mutane,” a cewar jam’iyyar.

Jam’iyyar tayi kira ga hukumar zaben ta INEC ta yi duk abin da wajaba don ganin an yi adalci ga sauran ‘yantakarar da suka shiga zaben su 10 ciki har da dantakarar jam’iyyar PDP.

Har ila yau jam’iyyar ta bukaci ganin hukumomi sun gudanar da bincike kan wannan rahotanni na yin karantsaye ga dokar zabe, a hukunta masu laifi don kare aukuwar hakan a nan gaba.

Jam’iyyar ta kuma bukaci kungiyoyi na sa kai da kafafan yada labarai da masu sa idanu kan harkokin zabe su ci gaba da sa idanu su fito da abubuwan da aka yi na kuskure, don kaucewa hakan anan gaba.

Kazalika jam’iyyar ta kara jaddada goyon bayanta ga mutunta dokar kasa da shigar da al’umma wajen tafiyar da gwamnati.

A karshe jam’iyyar ta PDP ta bukaci sauran masu ruwa da tsaki musamman daga jam’iyyar APC su yi fatali da tada hankula da barazana da sauran abubuwan da ke zama bana dimukuradiyya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwankwaso ya yi tsokaci game da zaben cike gurbi da akai a Kano

Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana...

A Hukuma ce INEC ta bayyana sakamakon zabukan cike gurbi da aka yi a kano

Hukumar zabe mai zamanta ta Kasa ta bayyana Dan...

Jam’iyyar APC ta bayyana matsayarta kan zaben cike gurbi a Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zabe:An kama ƴandaba sama da 100 da ake zargi da yunkurin tada tarzoma a Kano – INEC

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta...