Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya yi wata ganawar sirri da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar litinin .
Kadaura24 ta rawaito Kwankwaso ya gana da Shugaba Tinubu Jim kadan bayan da Kwankwaso ya halarci bude taron tattalin arziki da aka gudanar a babban dakin taro na fadar gwamnati, Abuja.
Wannan dai shi ne karo na biyu da kwankwaso da Tinubu su ka kulle Kofa a cikin shekaru biyu.

Ganawar da suka yi ta karshe a fadar Aso Rock Villa ita ce wadda suka yi a ranar 9 ga watan Yuni, 2023, kwanaki kadan bayan rantsar da Tinubu, wanda hakan ya sa Kwankwaso ya zama dan takarar shugaban kasa na farko da ya ziyarci shugaban kasa.
Babbar Kotun Tarayya ta kori karar da APC ta shigar kan hana biyan kuɗaɗen kananan hukumomin Kano
Da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa, Kwankwaso ya ce ya ce sun tattauna da shugaban kasa kan harkokin da suka shafi siyasa da mulki.
Ya kuma ce akwai yuwuwar ya yi aiki da Tinubu, amma bai yi cikakken bayani ba.
Duk da cewa ba a yi wa yan jaridu cikakken bayanin zaman ba, ziyarar ta Kwankwaso na zuwa ne makonni kadan bayan da aka kaddamar da hadar yan adawa wato jam’iyyar ADC hadakar da aka samar da ita domin kalubalantar Tinubu da jam’iyyar APC a zaben 2027.
Majiyoyin fadar shugaban kasa da aka tuntuba game da batun tattaunawar Tinubu da kwankwaso ba su bayyana abubuwan da mutanen biyu suka tattaunawar ba.
Wata majiya ta ce an gudanar da ganin ne a gidan shugaban kasa, inda ko hadiman shugaban kasar ma ba a bar sun sun shiga ba.