Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Wani Malamin addinin musulunci a kano Mai suna Dr. Aminu Isma’il Sagagi ya bukaci Matasa su rika neman Ilimin addini da na zamani tare da hadawa da sana’a don inganta rayuwarsu.

“Abun damuwa ne yadda a wannan zamanin mutane su ka fi fifita Ilimin boko akan na addini, kuma ake yiwa Mai Ilimin addini kallon hadarin kaji, tabbas Wannan ba daidai bane kuma ya Zama dole mu gyara”.

InShot 20250309 102512486
Talla

Dr. Aminu Sagagi ya bayyana hakan ne yayin wani taron da kungiyar Cigaban Ilimi ta unguwar Zango dake karamar hukumar birnin Kano suka shirya.

“A matsayinmu na Musulmi dole ne mu nemi Ilimin addini musulunci domin shi ne wanda zai taimakemu a lahira saboda da shi ne za mu San Allah da kuma yadda za mu bauta masa”.

Ya ce neman Ilimin addinin musulunci ba zai Hana neman Ilimin zamani ba ko sana’a ba, don haka yake shawarta Matasa da su hada uku komin wanne na da muhummci a rayuwar Dan Adam.

Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari

Dr. Sagagi ya ce ba daidai bane mutane su rika zarmewa wajen neman Ilimin boko kadai ba tare da hadawa dana Ilimi ba, inda ya ce hakan na da illa sosai.

Ya yi bayani Sosai musamman kan yadda matasa za su raba lokacinsu wajen neman ilimin addinin da na boko da kuma kasuwanci don samun kowana bangare.

Ya kuma yi tsokaci akan matasan da suke harkar daba da kuma yara da suke tasowa masamman na unguwar zango da kofar mata da yadda iyaye za su jajirce dan tarbiyantar da su domin gojewa harkar daba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu Ta Ɗage Sauraron Ƙarar DA ICPC ta Kai Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Jihar Kano

    Babbar kotun tarayya mai lamba shida(6) dake Babban Birnin...

Kisan ɗalibai a Kano: Kwamitin Malamai da Iyayen yara na jihar ya nuna damuwarsa

Daga Abdulhamid Isah D/Z Malam Salisu Abdullahi shugaban kwamitin malamai...

Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari

  Rahotanni daga Katsina na cewa gwamnan jihar Katsina Dikko...