Daga Abdulhamid Isah D/Z
Malam Salisu Abdullahi shugaban kwamitin malamai da iyayen yara na jihar Kano ya bayyana bacin rai da kuma takaicinsa bisa abin da ya faru a wata makarantar Sakandare a garin Bichi dake Kano inda aka zargi wasu dalibai da kashe yan uwansu dalibai 2.
Malam Salisu Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 a Kano .

Ya ce” Tabbas Wannan abun da ya faru akwai sakaci na iyaye na Rashin kulawa da Hakkokin da yake kan su na kulawa da ya’yan su wajen ba su cikakkiyar tarbiyyar bisa koyarwar musulunci .
“Insha Allahu Kwamitin iyayen Yara na jihar Kano yana matukar kokarin wajen bibiyar wannan lamari da kuma sake ɗaukar mataki na ganin irin wannan ba ya sake faruwa ba”. Inji Malam Salisu
Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari
Ya kuma yi kira ga duk wani dan kishin jihar Kano da ya taimaka wajen ba su bayanai na duk abin da suka gani da ga Dalibai na rashin ɗa’a kuma a shirye suke su dauki matakin gaggawa .
Ya kuma mika sakon godiya ga zabben Gwamna jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf bisa irin goyon bayan da ya ke ba su a kowanne lokaci.
A karshe ya mika sakon godiya ga Rundunar yansanda ta jihar Kano bisa irin kokarin da su ke yi wajen tabbatar da tsaro a jihar Kano .