Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar Juma’at nan 18 ga watan yuli 2025.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24.

Sanarwar ta ce dhugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai kawo ziyayarar ne domin yin ta’aziyyar marigayi Alhaji Aminu Dantata wanda ya rasu a baya bayan nan.
Zargin kwace gona: Majalisar Dokokin Kano zata binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada (ALGON)
Sanarwar Ta kuma bukaci alu’mmar jihar kano da su kasance masu karamci kamar tadda suka saba wajen nuna dattako da karbar bakuncin Shugaban kasar a gobe juma’a.
Tun bayan Rasuwar Marigayi Alhaji Aminu Dantata Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu bai samu damar zuwa Kano ba, Sai Gobe, amma dai Mataimakin sa Kashim Shettima ya zo amadadinsa.