Yadda mu ka yi da Buhari kwana daya kafin rasuwarsa – Mamman Daura

Date:

 

 

Alhaji Mamman Daura, ɗan uwan marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana ganawa ta ƙarshe da ya yi da tsohon shugaban ƙasar gabanin ƙarewar kwanakinsa a duniya.

A wata hirarsa da Jaridar This Day, Mamman Daura ya ce yana tare da Buhari a ranar Asabar da ta gabata kuma har an fara shirye-shiryen dawowarsa gida Nijeriya.

InShot 20250309 102512486
Talla

“Mun yi hira sosai da shi kan abubuwa da dama har da dariya kuma yana sa ran za a sallame shi ya dawo gida [Nijeriya] a wannan makon.”

A cewar Mamman Daura, marigayin ya buƙaci a tabbatar da biyan kuɗin masaukin duk waɗanda suka je duba shi yayin da yake jinya a Landan saboda har an soma batun sallamarsa daga asibiti.

Mamman Daura ya ce ya bar Buhari wanda ya soma murmurewa a asibitin da yake jinya da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar Asabar, da zummar dawowa washegari da safiyar Lahadi saboda likita zai sake bincikar lafiyarsa a wannan rana.

Halin da ake ciki game da shirin jana’izar Buhari

“Na baro shi da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Asabar. Yana cikin ƙoshin lafiya da tsammanin zai ga likitansa da safiyar ranar Lahadi.

“Sai dai zuwa tsakar ranar Lahadi, rashin lafiyar tsohon shugaban ƙasar ta ƙara tsananta, inda numfashinsa ya riƙa ɗaukewa, kuma duk da ƙoƙarin likitoci na ceto ransa, zuwa ƙarfe 4:30 na yammaci wa’adinsa ya cika.”

Kadaura24 ta ruwaito cewa, tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya riga mu gidan gaskiya a ranar Lahadin da gabata, inda a wannan Talatar za a yi jana’izarsa a garin Daura da ke Jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin kwace gona: Majalisar Dokokin Kano zata binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada (ALGON)

    Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha alwashin gudanar da...

Tinubu ya yi wa Buhari abun da Buharin ya kasa yi wa kakana- Jikan Shagari

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Nura Muhammad Mahe, jikan tsohon shugaban...

Yanzu-yanzu: Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fice daga...

Gwamnatin Jihar Kano ta fara bincike kan mutuwar wasu ɗaliban makarantar Sakandare biyu

  Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Makoda, ya...