Tuni shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya Isa jihar Katsina domin Karbar Gawar tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da halartar jana’izar Gawar a gidan Marigayin dake Daura.
Mintina Kadan bayan Isa shugaban Kasar , sai ga jirgin mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima ya sauka a Katsina tare da kawar Muhammadu Buhari .

Yanzu haka dai kowanne lokaci daga lokacin hada Wannan Rahoton za a iya wucewa da gawar mamacin domin yi masa sutura .
Da a asibitocin Nijeriya Buhari ya yi jiyya da tuni ya daɗe da mutuwa – Adesina
Tuni dai manya-manya mutane a ciki da wajen Nigeria suka Fara Isa Garin Daura domin halartar jana’izar Muhammadu Buhari.
Tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar da Nasiru El-rufa’i da Rotimi Amechi, Aminu waziri Tambuwal da wasu daga cikin Sarakunan Arewacin Nigeria duk sun Isa gidan Buharin domin halartar jana’izar Buhari.