Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar matuka manyan motoci reshen jihar Kano dake kofar kwanar singa a titin IBB, sun jaddada kudirinsu na kara inganta guraren tsayawarsu na din-din-din domin kaucewa Ambaliyar ruwa duba da wannan lokaci na damuna.
Shugabanin kungiyoyi biyu Aminu Alhasan Abubakar da Maikudi Usman Mai lodin Damaturu ne su ka jaddada hakan a lokacin da kungiyoyi biyu suka shirya taron manema labarai a kano .
Shugaban kungiyar kurkura ta kasuwar singa Aminu Alhasan Abubakar Wanda suke tsayawa a kusa da kofar a madadin ‘yankungiyarsa ya bayyana cewar, Kungiyar ta gudanar da aikace_aikace na yashe magudanan ruwa a yankunan shiga cikin kasuwar hadin gwiwa da Kungiyar matuka manyan motoci employee domin ganin sun marawa kungiyoyin dake cikin kasuwar singa da kewaye da Kuma, Gwamnatin jihar Kano na tsaftace lungu da sako na jihar Kano, musamman kasuwanni da tashoshi.

Shugaban kungiyar korkurar yace, sun Yi amfani da motocinsu wajen kwashe duk wani dagwalo da yake sanyawa ruwa gudu a dukkannin yankunan shiga cikin kasuwar singa.
Shugaban kungiyar ya ce ba za su gajiya ba wajen taimakawa yunkurin gwamnatin jihar Kano na tsaftace lungu da sako na jihar, Wanda yanzu haka injiniya Abba Kabir Yusuf ya sanya aikace-aikace ake yi ba dare ba rana.
Aminu Alhasan ya bayyana cewar, Kungiyar tana nan ta na shirin aiwatar da wani gagarumin aiki da zai rage yawan cinkoson ababen hawa a ciki da wajen kasuwar singa da kewaye, Inda Kuma shugabanin kungiyoyi biyu su ka yabawa hwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf da shugaban kungiyar SIMDA barista janaidu zakari da shugaban kungiyar AMATA bisa gudunmawar da suke Basu a kodayaushe domin an bunkasa kasuwanci da sufuri ga wadanda suke sana’oinsu a kasuwar singa.
Aminu Alhasan Abubakar ya yi kira ga direbobin kurkurar da su ci gaba da baiwa Gwamnatin jihar Kano da sauran kungiyoyin kasuwar singa hidin kan da suka kamata duba da goyan bayan da suke bayarwa.
A jawabinsa sakataren kungiyar manyan motoci reshen jihar dake Ibrahim tayo maikudi Usman Mai lodin Damaturu, ya bayyana cewar, kungiyoyinsu dake kofar shiga kasuwar singa ta yamma suna iya kokarinsu a fannin tsaftace mahallin filin gurin da suke tsayawa domin bunkasar sana’ar ta yau da kullum.
Maikudi Usman yace, ko a jiya ma sai da suka hadu tare da yashe magudanan ruwa da suka toshe domin ganin sun tsaftace mahallin filin gurin da suke tsayawa.
Daga karshe ya bukaci Gwamnan jihar da ta taimakawa duk Wadanda suke yunkurin wajen tsaftace mahallinsu da ma kawo dauki domin cinkoson ababen hawa a hayar Ibrahim tayo anan birnin Kano.
Sakataren kungiyar ya yabawa Gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa yadda ya sanya aka farfashe titina domin ganin an ingantasu da yin sabbi Wanda hakan ba Karamar nasara ba ce wajen ci gaban al’ummar jihar.
Maikudi Usman ya bayyana cewar kungiyoyinsa ta employee tana mika sako ta’aziyya ga Gwamnatin jihar Kano da masarautar Kano da iyalan murigayin Alhaji Aminu Alhasan Dantata, bisa rasuwar babban Dankasuwa Alhaji Aminu Alhasan Dantata daya rasu ya na da shekaru 94 a duniya.
Daga karshe ya yi kira ga yankungiyar employeer reshen kasuwar singa, da su jajirce kamar yadda suka Saba wajen tsaftace mahallinsu da Kuma taimakawa na rage cinkoson ababen hawa a titin IBB da sauran guraren dake cikin kasuwar singa da kewaye.