Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Date:

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen

Gwamnatin jihar kano ta umarci al’ummar jihar musamman matasa da yan bijilanti da su tashi tsaye domin kare kansu daga hare-haren yan daba da masu kwacen waya, wanda suka addabi al’ummar jihar musamman kananan hukumomin kwaryar birni da kewaye.

“Yanzu ba lokaci ne da matasa da yan bijilanti za su rika jin tsoro ko gujewa yan daba da masu kwacen waya ba ne, dole matasa su kare kansu da iyalan su daga wannan barazana ta masu kwacen waya da aikin daba”.

InShot 20250309 102512486
Talla

Kwamishinan tsaro na jihar, AVM Ibrahim Umar, mai ritaya, ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai, yayin da ya kai ziyarar jajantawa al’ummar Tudun Fulani da Kurna, akan yadda fadan daba yake janyo asarar dukiyoyi da rayuka, sakamakon kisan wani mutum a yankin.

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Kwamishinan ya kara da cewa kamata yayi kowa ya bayar da tasa gudunmawa wajen magance matsalar, ba wai a tsaya ana zagin gwamna a kafar zada zumunta ba, inda yace lokaci ne da za’a yi maganin yan daba in sun kawo farmaki.

IMG 20250415 WA0003
Talla

kwamishinan ya umarci matasa su yi maganin yan daba a duk lokacin da suka kawo hari, inda ya nemi a koyawa bata garin hankali kafin yan sanda su zo.

Daga karshe kwamishinan ya yabawa jami’an yan sanda akan yadda suka kama mutanen da suka aikata kisan kai ga wani mutum a yankin Tudun Fulani da Kurna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ga Duniya baki daya – Shugaban kamfanin Yahuza Suya

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Shugaban kamfanin Yahuza Suya & Catering...