Daga Ibrahim Aminu Riminkebe.
Al’ummar garin Gamar kwari dake yankin karamar hukumar Fagge a nan jihar Kano da safiyar ranar talata ne al’ummar garin mazan su da matan su har ta da kananan yara ba’a bar su a baya ba wajan gudanar da wata zanga zangar luma a cikin Garin na Gamar kwari.
Tunda fari dai mazauna garin sun gudanar da zangar ne biyo bayan zaban sabon Dagacin garin a sakamakon rasuwar tsohon Dagacin garin Alhaji Adamu Yusuf, Wanda Kuma bayan shiga zaban ne tsakanin Malam Kabiru Adamu Yusuf ya kuma samu kuri’u 87 yayin da abokin takarar sa Mai suna Rabi’u Saleh ya samu kuri’u 70 nan take suka taya junan su murna tare da yin fatan alkhairi.
Zaban da mazauna garin na Gamar kwari ke bayyana cewar an gabatar dashi a gaban masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Fagge cikin kuwa har da wakilin Hakimin karamar hukumar ta Fagge an Kuma tabbatarwa da al’ummar garin nan bada jimawa ba za’a saka rana Domin bikin nadin Sabon Dagacin garin.
To, amma Kuma kwatsam sai al’ummar garin suka samu wata sanarwa daga Hakimin karamar hukumar ta Fagge Kan cewar waccan zaban da aka gabatar sai an sake yin sa a Ranar larabar nan, suka Kuma kara da cewar ba a fada musu dalilin sake zaban ba duk da cewar kowa ya san Malam Kabiru Ado Yusuf shi ne yayi nasarar.
Majiyar Kadaura24 ta bayyana cewar sun bi dukkanin wata hanya daya kamata domin kamo bakin zaran alamarin Amma Kuma hakan bata samu ba, a dan haka ne al’ummar garin Gamar kwari suka yanke shawarar gudanar da waccan zanga-zangar lumar Domin janyo hankaulan mahukuntan dan daukar matakin daya kamata
Wakilin Kadaura24 yayi kokarin jin ta bakin bangaran wadanda aka yiwa wancan zargin akan su wato Hakimin karamar hukumar Fagge da kokarin yin mi’ara koma baya akan zaban Dagacin garin Gamar kwari to Amma har kawo zuwan wannan lokacin da muka hada wannan rahotanni bamu samu amsa daga bakin sakataran sa duk irin alkawarin dashi sakataran yayi mana na cewar zasu mai da martani akan wannan batu Amma Kuma shiru kake ji, zamu cigaba Bibiyar wannan batu da zarar sun magantu zaku jimu dasu.
Wannan zancen ba haka yake ba.
Na farko dai anyi zabe a garin Gama kwari, kuma wanda yaci shine kabiru Yusuf, to amma kafin a fara zabe Hakimi ya zayyano wasu dokoki na masarautar jihar Kano. Dokokin sune kamar haka:-
1- Dole ne mutum ya zama yana da ilimin Addini.
2- Dole ya kasance kana da takardar sheda kammala karatun secondary.
3- Dole mutum ya zama baya shaye-shaye.
To duk wadannan dokoki wancan wanda yayi nasara ya karyasu, sabo da bashi da ilimin addini kuma bashi da tarkardar shedar kammala karatun secondary, sannan yana shaye-shayen. Bayan bincike da akayi sai aka gano takardarma ta karya yaje akayi masa, ya kaita gidan sarki a fadar masarautar Kano ya karyata kansa yace ba tasa bace.
Daga nan shine aka dakatar da zaben kuma aka sokeshi, bayan wasu kwanaki sai sanarwa ta fito daga masarautar Kano cewar wannan zabe da akayi an sokeshi bisa wadancan sharuda da masarauta ta gindayasu kuma ya karyasu, kuma shi Kabiru an cireshi daga jerin ‘yan takara, tunda an sameshi da wadannan laifuka.
Daga nan sai Hakimi yace sai dai su kawo wani dan takarar, shine sai aka kai kanansa jiya talata 30/11/2021. To Hakimi yace zai tantance wadanda aka kawo yanzu domin a wancan zaben an samu kura-kurai, shine jiya Hakimi ya tantance su kuma yace yau laraba 01/12/2021 zaiyi zaben, jiya bayan an dawo daga secretary said kawai suke cewa Hakim ya munafurcesu kuma bazasu yarda ba. Shine sai suka fito kan titi suka tare suka fara yin kone-kone, suna cewa:- ” Jaba ba chanji sai Kebi kuma dole a basu abinda suka zaba”.
To wanna shine gaskiyar al’amari kuma shine abinda ya faru, to amma su sun maida abin political issue, kuma wannan ba haka bane.
Kai mai jaba kaji tsoran Allah , Kai kafi mahukunta ne sani dakabarsu sunmaganto kamar yadda jaridar kadaura tawallafa. Amma bakazo kana fadar abinda bashi da makama balle tushe , idanma duk wannan karyar dakayi gaskiya to kabari suzu sufadamana hakan tunda koyasan mune asalin Yan anguwar jaba. Inamai sanardakai dakakiya Yi bakinka .
Lallai Mai Jaba kacika makiri wlh kaida baka garinma Ina kasami wannan bayanin ,bayan wadanda suke garinma sunkasa cewa komai ,saikai Yakama mutum yarika cire son zuciya yafadi gaskiya ,,idankuma bahakaba kayi shiru yafima Alkhairi Amatsayinka na musulmi