Gwamnatin Kano ta fitar da al’ummar mu daga Matsalar Ruwan Sha – Shugaban K/H Gabasawa

Date:

Daga Surayya Malam Abba
Shugaban Karamar Hukumar Gabasawa da al’ummar yankin sun yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa Aikin Samar da Rijiyoyin Burtsatse Masu Amfani da hasken rana Guda buyu da aka gudanar a yankinsu.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Mahe Garba Garun Danga ya baiyana hakan ne Lokacin kaddamar da Sabbin Rijiyoyin Burtsatse Guda 2 da aka gudanar a Karamar Hukumar sa bisa sahallewar Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano.
Shugaban Karamar Hukumar yace ya Zama wajibi su yabawa Gwamnatin Saboda Aikin Zai fitar da dumbin al’umma daga Matsalar Ruwan Sha da Kuma inganta Lafiyar su.
Yace an gudanarwa da aikin Rijiyoyin Burtsatse ne a Garuruwan Garun Danga da Kwazari duk a Karamar Hukumar ta Gabasawa.
Alhaji Mahe Garba yace an Kashe Sama da Naira Miliyan 21 waje Gina Rijiyoyin Burtsatse Masu Amfani da hasken rana, Wanda ya baiya hakan a Matsayin Wani yunkuri da Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Kwamishina Kananan Hukumomi Alhaji Murtala sule Garo ke yi don fitar da al’umma daga dukkanin Wata Matsala.
Ya bukaci al’ummar garurun da aka gudanar da Aikin da su baiwa Aikin kulawar data dace domin su Dade Suna Amfana da Aikin,tare Kuma da yi musu alkawarin sake kai musu Wasu aiyukan da zasu inganta Rayuwar su.
 A nasu jawabin, Manyan limaman garurun Garun Danga da Kwazari Malam Waliyillah Muhd da Malam Abdullahi Musa sun godewa Kwamishina Murtala sule Garo da Shugaban Karamar Hukumar bisa Aikin Rijiyoyin Burtsatse da aka yi musu Wanda suka ce sun dade Suna bukatarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...