Daga Isa Ahmad Getso
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin wadda ba ta da sauran wani tasiri a fagen siyasar kasar, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ta mutu, abin da ya rage kawai abinne ta.
Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne yau Talata a Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin kungiyar goyon bayan Tinubu a wata ziyarar ban girma da su ka kai masa a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa.

A cewar tsohon gwamnan jihar Kano, jam’iyyar NNPP tana kan kafafunta na ƙarshe kuma karshenta ya kusa.
Acewar Ganduje, ƙofar shugabancinsa a buɗe take domin yin sulhu kuma zai yi maraba da dawowar Kwankwaso cikin APC idan har ya yanke shawarar komawa jam’iyyar ta APC.
Ganduje ya kara da cewa “Shi wancan da ke kiran kansa da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, ba mu da matsala da shi don ya ce zai dawo APC, za mu karbe shi kuma mu yi masa maraba.