Shugaban kamfanin Fauza General Enterprise ya mika ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi

Date:

Daga Saminu Ibrahim Matashi

 

Shugaban kamfanin Fauza General Enterprises dake jihar Kano Alhaji Alhasan Aliyu, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano kuma babban dan majalisar masarautar Kano, Alhaji Abbas Sunusi Bayero, wanda ya rasu yana da shekaru 92 .

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban kamfanin Fauza General Enterprises ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

InShot 20250309 102403344
Talla

“Ina mika sakon ta’aziya ta ga Shugaban Jam’iyyar APC na Kano Alh. Abdullahi Abbas bisa rasuwar mahaifinsa Galadiman Kano Alh. Abbas Sunusi, Allah ya gafarta masa”. Inji Alh. Alhassan Aliyu

Shugaban Kamfanin Fauza General Enterprise ya bayyana marigayi Galadiman Kano a matsayin wani dattijo mai daraja wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban Kano da kuma sha’anin sarauta a arewacin .

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranakun komawa makaranta

“Rasuwar Alhaji Abbas Sunusi babban rashi ne, ba ga iyalansa kadai ba, har ma ga daukacin Masarautar Kano da kuma al’ummar jihar baki daya, domin mutum ne mai hikima da rikon amana, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al’umma.” Inji shugaban kamfanin Fauza

Alhaji Alhasan Aliyu , ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashin.

“Ina mika ta’aziyyata ga Abdullahi Abbas shugaban jam’iyyar APC na Kano da daukacin iyalan Galadima, Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi Aljanatul Firdaus,” Inji Zaura

Idan za a tunawa Kadaura24 ta rawaito Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sunusi rasuwa a daren ranar Talata, inda ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.

An haife shi a shekarar 1933 a garin Bichi na jihar Kano, ya taba zama Wamban Kano kafin Sarki Sanusi Lamido Sanusi ya nada shi sarautar Galadiman Kano a shekarar 2014.

Galadiman Kano ya ba da gudunmawa sosai wajen cigaban harkokin Masarauta da abubuwan da suka shafi shugabanci a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...