Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Date:

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a shirye yake ya yi aiki da Peter Obi domin samar da shugabanci na gari ga ‘yan Najeriya.

Bala Muhammed ya bayyana haka ne a Bauchi a ranar Alhamis lokacin da Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, a zaben 2023, ya kai masa ziyarar a jihar.

InShot 20250309 102403344
Talla

A cewarsa, ziyarar wadda ta ta’allaka ne kan yadda shi da Obi za su yi aiki kafada da kafada da juna don magance talauci, taa’addanci da sauran matsalolin Nigeria.

“Mun tattauna kalubalen da jihohi suke fuskanta, kuma na ji dadin abin da yake yi a matsayinsa na jagoran jam’iyyar adawa domin ko muna so ko ba mu so shi ne jagoran ‘yan adawa a Najeriya.

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

“Za mu tabbatar da cewa mun hadu wuri guda, mu hada karfi da karfe, mu samar da shugabanci nagari a kasar nan, mu ba da kyakykyawar adawa ta ilimi, da hangen nesa ta yadda za mu kwato kasarmu.

A jawabinsa Peter Obi ya ce kasar nan na bukatar zuba jari mai tsoka a muhimman wurare domin fitar da mutane daga kangin talauci domin a rage aikata laifuka a cikin al’umma.

Mista Obi ya yi ganawar sirri da Gwamna Mohammed ta fiye da sa’o’i uku kafin daga bisani su sanar manema labarai abubuwan da suka tattauna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...