Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Karamin Ministan gidajen da raya burane na Nigeria Yusuf Abdullahi Ata ya ce matukar aka sake baiwa Abdullahi Abbas ko irinsa Shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano sai sun fice daga jam’iyyar.

“Muna gayawa kowa indai aka mayar da su billahillazi duk irin mu fita za mu kuma sai jam’iyyar ta sake faduwa. Irin wadannan mutanen ba ma tare da su kuma ko me za a yi mu bama tare da su, su na aiko mana da sako mu ma mu na aika musu da sako”.

Karamin Ministan na ya bayyana hakan ne yayin wani taro da yayi da mutanesa a Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya ce irin kalaman da Abdullahi Abbas ya yi na tuhumar Allah da izgili sune suka kayar da jam’iyyar APC a zaben shekara 2023 , kuma ya ce muddin aka sake baiwa Abdullahi Abbas shugabancin APC a Kano ba makawa sai jam’iyyar ta sake faduwa.

” Mu an yi mana tarbiyya mun san waye Allah, mun san waye malami mun kuma san waye babba, saboda haka ba za mu sauka daga tarbiyyar mu ba, in aka kuma sa su za mu fita kuma wallahi jam’iyyar sai ta sake faduwa”. Inji Ministan

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Yusuf Abdullahi Ata ya ce dole ne a chanza su Abdullahi Abbas a kawo mutanen kirki masu mutunci , saboda Allah ya sake baiwa APC mulkin jihar Kano, domin Allah ya shi yake ba da mulki ba yawan kuri’a ba.

“Kuri’a ba ta ba da mulki ba, kudi ba zai ba ka mulkin ba , al’umma ba za su ba ka mulki ba , ai an zabi Gawuna da Garo kuma su suka ci zabe clean, amma Allah ya ba da dama aka yi mana magudi kuma mu ka je kotu aka tantance aka gano an yi mana magudi, amma daga karshe mai bayarwar sai ya hana mu saboda mun kalubalance shi”. A cewar Ata

Wannan dai shi ne karon farko da Ministan ya fito yana irin wadannan kafafan kalaman akan jagororin jam’iyyar APC a Kano. sai dai ana ganin hakan ya samo asali ne da yadda jagororin jam’iyyar suka nuna adawarsu da atan lokacin da aka nada shi a matsayin karamin ministan gidajen, bayan da shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire Abdullahi Tijjani Gwarzo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...

Za mu kashe Sama da Naira miliyan 105. Dan Bunkasa Harkar ilimi a karamar hukumar Dala – Hon Surajo Imam

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Surajo...