Kwanaki 100: Shugaban karamar hukumar Wudil ya kaddamar da wasu aiyukan raya kasa

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Shugaban karamar hukumar Wudil, Alhaji Abba Muhammad Tukur Utai, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da ayyukan raya kasa da cigaban al’ummar karamar hukumar.

Abba Muhammad Tukur ya bayyana haka ne a yayin bikin cikarsa kwanaki dari na farko a kan karagar mulki, inda ya bayyana niyarsa ta inganta walwala da ci gaban al’umma a garin Wudil.

Shugaban karamar hukumar Wudil Alhaji Abba Muhammad Tukur Utai ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka tare da aza har sashin ginin wasu aiyukan.

InShot 20250115 195118875
Talla

Abba Muhammad Tukur Utai, ya mika godiyarsa ga gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar NNPP bisa goyon bayan da suke baiwa karamar hukumar Wudil.

A yayin taron, shugaban ya zayyana ayyuka da dama da aiyukan jin kai da tallafi da ya bayar da nufin inganta rayuwar jama’arsa.

A karon farko mace ta zama shugabar kungiyar Shugabannin kananan hukumomin Kano

Daga cikin aiyukan da gwamnatinsa ta yi akwai ginin daki tsaro da aka samar a mashigar garin wudil domin magance matsalolin tsaro, sannan an samar da rijiyoyin burtsatse da dama a kauyuka daban-daban da kuma samar da kayan daki ga Wasu amare.

Ya kuma kara da cewa Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da bayar da kudade don kara gudanar da wasu muhimman ayyuka da suka hada da gina karin rijiyoyin burtsatse da ayyukan hanyoyi da dama a garuruwa daban-daban, yayin da a bangaren kiwon lafiya kuma za a gina wasu sabbin asibitoci guda biyu, tare da karin kayayyakin kiwon lafiya da makarantu.

Duk sati ana hada-hadar Naira biliyan 50 a kasuwar shanu ta Wudil – Shugaban kasuwar

Bugu da kari, shugaban ya bayyana cewa yanzu haka ana gyaran wasu azuzuwa a makarantu daban-daban da kuma samar da karin ababen more rayuwar al’umma a karamar hukumar.

Shugaban ya kuma bayyana cewa an shirya don fara shirin kula da lafiyar ido kyauta ga al’ummar garin Wudil, inda ya jaddada kudirin majalisar karamar hukumar na inganta rayuwar al’umma baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Karamin Ministan gidajen da raya burane...

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...