Zargin Badala: Gwamnatin Kano ta dakatar da daukar wani Fim

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

A kokarinta na tsaftace finafinan da ake yadawa a tsakanin al’umma, hukumar tace finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta dakatar da wani shiri Mai suna ‘Zarmalulu’ tare da gayyatar dukkannin wanda suka fito a cikinsa domin jin ba’asi biyo bayan zargin da akai mata kan mashirya shirin da bai dace ba da kuma yin amfani da Kalmar badala a matsayin sunan shirin.

Biyo bayan korafe-korafe da Hukumar ta karba daga wasu yan kishin Jihar Kano akan shirin, Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya bayyana damuwarsa akan alamurin tare da dakatar da film din haka kuma, Abba El-mustapha ya gayyaci dukkannin wanda suka fito a shirin domin jin ba’asi na yin amfani da ita kalmar.

InShot 20250115 195118875
Talla

Shirin mai suna “Zarmalulu” ana zarginsa da rashin ma’ana tare da kama da wani suna na badala a saboda da haka Hukumar ta dakatar da shi tare da kira ga dukkannin wanda suka fito a cikinsa dasu bayyana a gaban kwamatin da Hukumar ta kafa wanda kin yin hakan ka iya jawowa mutum fushin Hukumar.

Al’ummar unguwar Kan Tudu Sun yabawa Gwamnan Kano bisa Nada Waiya A Matsayin Kwamishina

Sanarwar wacce mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani ya aikewa Yan Jaridu, ta ce hukumar na da hurumin kan dakatar da dukkannin wani shiri da bata gamsu da yadda aka shirya shi ba tare da laddaftar da duk wani da ta samu da yin abinda bai kamata a cikin kowanne shiri da ake yadawa jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar samarin Tijjaniyya ta yi Allah – wadai da hukuncin Kotun ECOWAS

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Kungiyar Samarin Tijjaniya ta kasa tace...

Majalisar dokokin Kano da Freedom Radio sun fara musayar kalamai

Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi al'ummar jihar Kano...

2027: Shugabannin APC a Kano ta Kudu sun mika bukatarsu ga Sanata Kawu Sumaila

Shuwagabannin jam’iyyar APC da Sakatarorin su na mazabar Kano...

Tinubu ya sake ƙaddamar da aiki titin Abuja zuwa Kaduna

Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gina...