Al’ummar unguwar Kan Tudu Sun yabawa Gwamnan Kano bisa Nada Waiya A Matsayin Kwamishina

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Al’ummar unguwar Kan Tudu dake karamar hukumar Dala a jihar Kano sun yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa nada Kwamared Ibrahim Abdullahi a matsayin kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida.

Dattawa da matasa da kungiyoyin mata da ’yan siyasa dake unguwar ne suka hallara a yammacin ranar Lahadin nan don karrama kwamishinan bisa nadin da aka yi masa da kuma yadda yake aikinsa.

Shugaban jam’iyyar NNPP na karamar hukumar Dala, Alhaji Dayyabu Maiturare ya yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya nada wanda ya dace a matsayin kakakin gwamnati.

InShot 20250115 195118875
Talla

A bangarensa shugaban jam’iyyar NNPP na mazabar kan tudu Alhaji Abdulkadir Danladi Nasidi ya ce an shirya taron ne domin yin godiya ga gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ya nada dansu a majalisar zartarwarsa.

Ya ce, Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi fice a Kano da wajenta wajen fafutukar kare muradun talaka, ya na kuma nuna kwazonsa Kan aikin da aka dora masa.

Yanzu-yanzu: Gwamna Yusuf ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar Kano

Da yake mayar da martani, kwamishina Waiya ya nuna godiya ga al’ummar unguwar Kan Tudu da suka karrama shi, inda ya ba da tabbacin cewa zai hada kai da su wajen samar da ayyukan raya kasa da suka hada da tallafawa matasa da samar musu da aiyukan yi .

Ya kuma tabbatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso goyon bayan karamar hukumar Dala.

Kwamishinan ya bukaci al’ummar mazabarsa da su tura masu sukarsa da cewa shi ba dan siyasa ba ne, zuwa gidan Alhaji Uba Jigo wanda shi ne ubangidansa a siyasa.

Taron ya samu halartar ‘yan kasuwa da mata, Malamai, kungiyoyin matasa da ‘yan siyasa da dai sauransu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu Yanzu: Hukumar KNUPDA ta rushe gaban shagon jarumar Tiktok Rahama

Daga Rahama Umar Kwaru   Hukumar KNUPDA ta kaddamar da rushe...

Wata kungiya ta bukaci Gwamnan Kano ya dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Wata kungiya mai zaman kanta mai...

Kwankwaso ba zai koma APC ba – Buba Galadima

Kusa a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya karyata jita-jitar...

Yadda gwamnan Kano ya ke rabon kujerun aikin hajjin bana kamar gyada

Daga Rahama Umar Kwaru Al'ummar jihar Kano na cigaba da...