Daga Junaidu Saani
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a gudanar da babban taron jam’iyyar APC na Kasa a watan Fabrairun Shekara ta 2022.
Shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagudu ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja a ranar Litinin.
Taron ya kuma samu halartar shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC Mai Mala Buni wanda kuma shine gwamnan jihar Yobe da kuma gwamna Badaru Abubakar na Jigawa.
Atiku Bagudu, wanda bai bayyana takamaiman ranar da za a gudanar da babban taron a watan Fabrairu ba, ya ce an sauya Ranar taron ne saboda har yanzu jihohi hudu ba su kammala taronsu ba.
Ya ce: “A jiya, 21 ga watan Nuwamba, kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, inda muka yiwa kwamitin rikon godiya bisa kokarin da suka yi wajen jagorantar jam’iyyar. Mun kuma gode wa shugaban kasa da ya ba su goyon baya don cimma aikin da aka dora musu.