Buhari ya Amince a baiwa Kowacce Jiha tallafin Naira Biliyan 18

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da bai wa jihohin ƙasar 36 tallafin naira biliyan 656.112.

Bayanan tallafin sun fito ne yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya jagoranta ranar Alhamis.

Wata sanarwa daga ofishin Mista Osinbajo ta ce kowace jiha za ta samu naira biliyan 18.225, wanda za ta biya cikin shekara 30 kan kuɗin ruwa kashi 9 cikin 100.

A cewar fadar shugaban ƙasa, an ɗauki matakin ne saboda a tallafa wa jihohi cimma muradansu na harkokin kuɗi musamman kasafin kuɗaɗensu na shekara.

Za a raba kuɗin ne a mataki shida cikin wata shida kuma ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN) za a rarraba wa jihohin.

Tun a watan Yuli ne Ministar Kuɗi Zainab Ahmad ta faɗa wa majalisar cewa za a fara zarar kuɗi daga asusun jihohin domin fara biyan bashin tallafin farko da aka ba su, amma sai jihohin suka nuna turjiya tare da neman wani agajin, abin da ya sa aka ɓullo da agajin kasafin kuɗin kenan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...