Daga Safyan Dantala Jobawa
Sashin lafiya na karamar hukumar Garun mallam ya nemi hadin kan iyayen yara don samun nasarar aikin allurar rikafin cutar kyanda.
Mustapha Ahmad Gambo ya ce allurar rigakafin kyandar za ayi wa yara ‘yan watanni t 9 zuwa shekaru biyar 5 a ka’idance. Sannan ya bayyan wuraren da za a gudanar da aikin allurar a dukkannin asibitocin da ke yankin.
A karshe ya nemi sauran al’umma da su bada hadin kai kamar yadda ya kamata don samun yara Masu cikakkiyar lafiya yankin dama kasa baki daya.
A nasu jawaban daban-daban limaman yankin sun sha alwashi bada hadin kai tare da yin kira a cikin hudubobinsu don a Sami nasarar Shirin, haka zalika, sauran dagatai suma sun sh alwashin isar da sakon wayar da kai ga al’ummar su don samun wannan nasarar ta aikin allurar rigakafin cutar kyanda.