Rigakafin Kyanda: An Shirya taron wayar Kan Masu Ruwa da tsaki a K/H Garun Mallam

Date:

Daga Safyan Dantala Jobawa

 

Sashin lafiya na karamar hukumar Garun mallam ya nemi hadin kan iyayen yara don samun nasarar aikin allurar rikafin cutar kyanda.

Kadaura24 ta rawaito Shugaban sashin Alh Mustapha Ahmad Gambo ya bukacin hakan a wani taro na musamman wanda aka shirya tare da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Wanda aka gudanar a fadar Ajiyan Rano hakimin Garun mallam.
Ya ce sun bukaci hadin kan ne domin samun nasarar aiki wanda za a fara a ranar asabar 20/11/2021 wanda aikin allurar rikafin zai dauki kwanaki 6 ana aiwatarwa.

 Mustapha Ahmad Gambo ya ce allurar rigakafin kyandar za ayi wa yara ‘yan watanni t 9 zuwa shekaru biyar 5 a ka’idance. Sannan ya bayyan wuraren da za a gudanar da aikin allurar a dukkannin asibitocin da ke yankin.

A karshe ya nemi sauran al’umma da su bada hadin kai kamar yadda ya kamata don samun yara Masu  cikakkiyar lafiya yankin dama kasa baki daya.

 A nasu jawaban daban-daban limaman yankin sun sha alwashi bada hadin kai tare da yin kira a cikin hudubobinsu don a Sami nasarar Shirin, haka zalika, sauran dagatai suma sun sh alwashin isar da sakon wayar da kai ga al’ummar su don samun wannan nasarar ta aikin allurar rigakafin cutar kyanda.

A karshe Ajiyan Rano kuma hakimin Garun mallam Alh Lawan Abubakar Madaki ya godewa Sashin lafiya na karamar hukumar bisa irin namijin kokarin da su ke bai wa yankin ba dare ba rana.
 Mahalarta taron sun hada da daukacin Dagatai da manyan Limamai da saura masu ruwa da tsakin yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...