Gwamna Matawalle na Shirin rushe sakatariyar Jam’iyyar PDP a Zamfara

Date:

Daga Maryam adamu Mustapha
Jam’iyyar PDP ta ce ta shigar da kara tana kalubalantar Hukumar Tsara Birane ta Zamfara, ZUREP, kan batun rushe sakatariyar jam’iyyar ta jihar a Gusau.
 Bala Mande, shugaban riko na jihar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron Masu Ruwa da tsaki jam’iyyar a sakatariyar ranar Laraba.
 Bala Mande, wanda tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin zamfara ne Lokacin Bello Matawalle yace sanya alama a sakatariyar jam’iyyar domin rushe ta ba dai-dai ba ne kuma wani yunkuri ne na kuntatawa ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP a zamfara.
 “’ya’yan jam’iyyar PDP ‘yan kasa ne masu bin doka da oda, kuma mun tunkari kotun da ta dace domin neman hakkinmu kan lamarin.
 Shugaban rikon jam’iyyar PDPn, wanda Kanar mai ritaya ne, ya bukaci magoya bayan jam’iyyar PDP da su ci gaba da bin doka da oda, kuma su guji daukar doka a hannunsu.
 Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya rawaito cewa, a karar da aka shigar a gaban babbar kotun Zamfara da ke zamanta a Gusau, jam’iyyar PDP na daga cikin wadanda ke neman kotu ta yi watsi da Shirin  rushe sakatariyar jam’iyyar da ZUREP ke Shirin yi, Inda tasa alama tun a ranar 29 ga watan Oktoba tare da bayyana ginin sakatariyar a matsayin haramtacce.
Kadaura24 ta rawaito Gwamnan Jihar zamfara Bello Matawalle Bai Dade da barin jam’iyyar ta PDP ba ,Inda ya Koma jam’iyyar APC tun a Watan yuli Wannan Shekara.

18 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...